Barau Ya Yabawa Sojoji kan Kisan 'Yan Bindiga a Kano, Ya Mika Sabuwar Bukata

Barau Ya Yabawa Sojoji kan Kisan 'Yan Bindiga a Kano, Ya Mika Sabuwar Bukata

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya yi martani kan nasarar da dakarun sojoji suka samu kan 'yan bindiga a Kano
  • Sanata Barau ya yabawa dakarun sojojin kan nasarar da suka samu ta hallaka 'yan bindiga masu yawa yayin artabun da suka yi
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bukaci jama'an yankin da 'yan bindiga ke kai hari da suka kara lura wajen sanya ido kan motsin da ba su yarda da shi ba

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi tsokaci kan nasarar da sojoji suka samu kan 'yan bindiga.

Sanata Barau ya yaba wa sojojin Najeriya bisa nasarar da suka samu ta fatattakar ‘yan bindigan da suka kai hari a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Sanata Barau ya yabawa dakarun sojoji
Sanata Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Jaridar The Guardian ta tattaro cewa hakan na kunshe ne wata sanarwa da mai ba Sanata Barau shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi wa shugabannin al'umma 2 yankar rago a jihar Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kano

Sojojin hadin gwiwa karkashin Operation MESA, tare da jami’an tsaro na wasu hukumomi, sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga guda 19 a ranar Asabar.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan bindigan ne bayan fafatawa da su yayin da suka yi kokarin kai hari a karamar hukumar Shanono daga jihar Katsina.

Sai dai a yayin arangamar, sojoji biyu da ɗan sa-kai ɗaya sun rasa rayukansu yayin kare ƙasar daga wadannan miyagu.

Me Barau ya ce kan kisan 'yan bindiga?

Sanata Barau ya gode wa sojojin saboda jarumtarsu da jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“A ranar 1 ga Nuwamba, bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan bindiga, dakarun sojoji tare da wasu jami’an tsaro sun kai farmaki, inda suka hallaka ‘yan bindiga 19."
“Sanata Barau ya yaba da jarumtar dakarun da kuma yadda suka fuskanci miyagun cikin kwarewa."
"Ya kuma yi jaje ga iyalan sojoji biyu da ɗan sa-kai ɗaya wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare yankin.”

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yaba wa sojoji bisa nasarar da suka samu a Kano, ya tura sako ga Tinubu

- Isma'il Mudashir

Sanata Barau ya ba jama'a shawara

Sanata Barau da ke wakiltar Kano ta Arewa ya bukaci jama’an yankin su kasance masu sanya idanu, tare da sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani motsi da ba su yarda da shi domin daukar mataki cikin gaggawa.

Sanata Barau ya yabawa sojoji kan kisan 'yan bindiga
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro a karamar hukumar Shanono, yankin Kano ta Arewa, da jihar Kano baki ɗaya.

“Shanono da sauran kananan hukumomi a yankinmu suna cikin zaman lafiya, kuma ba za mu bari waɗannan miyagun da ke shigowa daga jihohi makwabta su zo su tada hankalin al’ummarmu ba."

- Isma'il Mudashir

Gwamna Abba ya yaba da kisan 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba kan nasarar da sojoji suka samu kan 'yan bindiga.

Gwamma Abba ya ce kokarin da jami'an tsaron suka yi na tunkarar yan bindigan a kan lokaci tare da kashe da dama daga cikinsu abin ya yaba ne.

Kara karanta wannan

Dan majalisar tarayya ya sha da kyar bayan 'yan bindiga sun kai masa farmaki

Hakazalika gwamnan ya yabawa dakarun sojoji bisa juriya da jarumtar da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng