Falana: Babban Lauya Ya Ba Gwamnatin Tinubu Shawara kan Batun Juyin Mulki

Falana: Babban Lauya Ya Ba Gwamnatin Tinubu Shawara kan Batun Juyin Mulki

  • Ana ci gaba da magana kan zargin yunkurin juyin mulki da ake cewa wasu sojoji sun yi don kifar da gwamnati
  • Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN, ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin
  • Femi Falana ya bayyana cewa bai kamata gwamnati ta ci gaba boyewa 'yan Najeriya gaskiyar abin da ya faru kan lamarin ba

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya yi tsokaci kan batun yunkurin juyin mulki.

Femi Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kasance mai fadin gaskiya ga ‘yan Najeriya dangane da rahotannin da ke yawo kan yunkurin juyin mulki da ake zargin sojoji sun shirya a kasar nan.

Falana ya ba gwamnatin Shugaba Tinubu shawara
Babban lauya Femi Falana da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @femifalana, @DOlusegun
Source: UGC

Babban lauyan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin “Politics Today” na Channels Tv a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Femi Falana: Babban lauya ya fallasa Trump kan zargin kisan Kirsitoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Falana ya ce kan yunkurin juyin mulki?

Femi Falana ya ce har yanzu gwamnati ba ta fito da sahihan bayanai kan rahotannin cafke wasu da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin ba.

Ya ce idan gwamnati ta bayyana gaskiya, zai taimaka mata wajen samun amincewar jama’a da goyon bayan su wajen yakar masu adawa da tsarin dimokuraɗiyya.

“Ka sani, akwai jita-jita masu yawa da ake yadawa yanzu, kuma ni a matsayina na lauya, zan yi magana ne kawai kan abin da na sani cikin bayanan da suka fito fili."
“A ganina, gwamnati tana samun karin kuɗin shiga daga sayar da mai. Bayan cire tallafin fetur, ta kuma kara yawan man da ake samarwa a kasar nan."
“Amma har yanzu yawancin ‘yan kasa suna cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki. Idan mutane za su shirya juyin mulki, sukan yi amfani da fushin jama’a don cimma burinsu”

- Femi Falana

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanin sojoji a cikinsu

Wace shawara Falana ya ba gwamnati?

Falana ya ci gaba da cewa, duk da gwamnati ta musanta yunkurin juyin mulki, bai kamata ta yi shiru ba kan kama mutanen da ake zargi ba.

Femi Falana ya ba gwamnati shawara
Babban lauya a Najeriya, Femi Falana Hoto: @femifalana
Source: Twitter
“Gwamnati ta ce babu wani yunkuri na juyin mulki. Amma a gani na, dole ne ta fito ta yi bayani cikin gaggawa, domin har yanzu ba ta musanta rahotannin kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin ba."
“Dole gwamnati ta kasance mai fadin gaskiya ga ‘yan kasa idan abin ya faru, ko idan an shirya shi amma bai tabbata ba. Ya zama wajibi ta fito da cikakken bayani.”

- Femi Falana

Femi Falana ya karyata Donald Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban lauya, Femi Falana, ya yi martani kan kalaman da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi kan Najeriya.

Femi Falana ya bayyana cewa Donald Trump ya yi karya kan Najeriya bisa zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

Kara karanta wannan

Tsohon darektan DSS ya tsoratar da Najeriya a kan barazanar Trump, ya bada mafita

Babban lauyan ya bayyana cewa 'yan ta'addan da ke kashe-kashe a Najeriya, ba sa tambayar addini kafin aikata ta'addancin su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng