Luguden Wuta a Najeriya: APC Ta Rubutawa Majalisar Amurka Wasika kan Trump

Luguden Wuta a Najeriya: APC Ta Rubutawa Majalisar Amurka Wasika kan Trump

  • Jam’iyyar APC reshen Amurka ta rubuta wa majalisar dokoki wasiƙa domin karyata cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya
  • Wasiƙar ta zo ne bayan barazanar shugaba Donald Trump na yi wa Najeriya luguden wuta bisa zargin kisan kiyashi kan Kiristoci
  • Shugaban APC ta reshen Amurka, Tai Balofin, ya ce zargin ya samo asali ne daga bayanan da aka cakuda domin biyan bukatun siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Reshen jam’iyyar APC na Amurka ya rubuta wasiƙa zuwa ga shugabannin majalisar dokokin ƙasar.

Wasikar ta buƙaci 'yan majalisar su da su yi hattara da labaran da ake yadawa kan zargin ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Bola Tinubu, Donald Trump
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta ce mataki ya biyo bayan barazanar Donald Trump, wanda ya ce zai iya tura sojojin Amurka zuwa Najeriya idan gwamnati ba ta dakatar da abin da ya kira “kisan Kiristoci” ba.

Kara karanta wannan

Trump: Najeriya ta gana da jakadun kasashe, an yi maganar Shari'ar Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasiƙar da aka rubuta a ranar 5, Nuwamba, 2025, APC ta bayyana cewa hanya mafi dacewa ita ce tattaunawa da hadin gwiwar diflomasiyya, ba yaki ko luguden wuta ba.

Kiran jam'iyyar APC ga majalisar Amurka

Wasiƙar, wadda Farfesa Tai Balofin ya rattaba wa hannu, an tura ta zuwa ga manyan shugabannin majalisar — Mike Johnson, Chuck Schumer, Hakeem Jeffries, da John Thune.

Shugaban APC na Najeriya
Shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Farfesa Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

A ciki, jam’iyyar ta ce tana girmama jajircewar Amurka wajen kare ‘yancin addini, amma ta gargaɗi cewa akwai “labaran da aka cakuda” da ke neman karkatar da gaskiyar halin da ake ciki a Najeriya.

Balofin ya bayyana cewa zargin kisan kiyashi da ake yadawa na iya zama ana yinsa ne saboda siyasar cikin gida a Najeriya, musamman saboda babban zaben 2027.

Jam'iyyar APC ta kare gwamnatin Tinubu

A cewar wasiƙar, duk da cewa ana samun tashin hankali a wasu yankuna, matsalolin sun fi alaƙa da rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya, ba wai kisan addini ba.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

The Guardian ta rahoto cewa APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna kishin kasa da adalci wajen magance matsalolin tsaro:

“Bayan harin da ya kashe mutane sama da 200 a jihar Benue, shugaba Tinubu ya ziyarci wurin, ya ba da umarnin kama wadanda suka aikata laifin, kuma a gurfanar da su bisa dokar ta’addanci da kisan kai,”

APC ta yi gargadi kan kawo hari Najeriya

APC ta ce irin rahotannin da aka kawo sun wuce gona da iri kuma suna iya lalata dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, tare da hana zuba jari da raunana hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.

Wasiƙar ta kara da cewa:

“Maimakon a dauki matakan soja, muna rokon majalisar dokokin Amurka da ta fifita hanyoyin diflomasiyya da hadin kai.”

Ta bayyana cewa hanya mafi inganci ita ce yin hadin gwiwa ta bangaren shari’a, shirye-shiryen tattaunawar addinai, da kuma haɗin gwiwa da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Amurka ta shirya kai hari Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka sun tsara matakan da za su bi wajen yaki da ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Ministan Tinubu, Keyamo ya tura budaddiyar wasika ga Shugaba Trump

Sojojin sun tsara cewa za su bi matakai uku wajen kai harin, wanda dukkansu za su bayar da damar nuna karfin soja.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka, Donald Trump ya dage da cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng