Gwamna Fintiri zai Tura Dalibai 100 Karatu Kasar Waje, zai Kashe Naira Biliyan 2.7

Gwamna Fintiri zai Tura Dalibai 100 Karatu Kasar Waje, zai Kashe Naira Biliyan 2.7

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.7 domin daukar nauyin dalibai zuwa kasar waje
  • Tallafin karatun zai kunshi fannoni hudu masu muhimmanci, ciki har da bangaren gine-gine, fasahar sadarwa da likitanci
  • An kuma amince da karin kudin aikin wutar lantarki a Jada da kuma horar da dalibai kan fasahar sola a kwalejin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta amince da daukar nauyin dalibai 100 ‘yan asalin jihar su yi karatun digirin PhD a kasar Turkiyya.

Hakan na zuwa ne bayan taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 22 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Yola, karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Farfesa Kaletapwa Farauta.

Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamna Fintiri yana jawabi a ofis. Hoto: Adamawa State Government
Source: Original

Hadimin gwamna Umaru Fintiri, Paul Barnabas ya wallafa a X cewa kwamishinan yada labarai, James Iliya ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa na so a ajiye motoci masu aiki da fetur a koma na lantarki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Adamawa zai tura dalibai karatu waje

A cewar James Iliya, shirin tallafin karatun na cikin kokarin gwamna Fintiri na bunkasa ilimi da gina hazikan matasa da za su kara wa jihar ma’aikata a fannoni masu muhimmanci.

Ya bayyana cewa wannan shiri zai bai wa daliban damar yin karatu a manyan jami’o’in kasar Turkiyya, domin samun kwarewar zamani da za su dawo su yi amfani da ita a gida.

Kwamishinan ya ce:

“Wannan mataki wani bangare ne na manufofin gwamnatin gwamna Fintiri na inganta rayuwar dan Adam domin samun ci gaba mai dorewa a jihar Adamawa.”

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Adamawa za ta kashe Naira biliyan 2.7 a shirin tura daliban karatu.

Fannonin da shirin karatun zai kunsa

Rahotanni sun nuna cewa tallafin karatun kasashen waje zai mayar da hankali ne a fannoni da suka hada da gine-gine, fasahar sadarwa, da likitanci.

An bayyana cewa za a zabi daliban ne bisa cancanta, domin tabbatar da cewa wadanda suka samu damar za su iya wakiltar jihar cikin kwarewa da mutunci.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta fara shirin tilasta koyarwa da harshen Hausa a makarantu

Shirin inganta lantarki a Adamawa

Haka kuma, majalisar ta amince da karin kudin aikin wutar lantarki na kauyukan So’o da Mapeo da ke karamar hukumar Jada da kimanin Naira miliyan 2.4.

Bugu da kari, an amince da kashe Naira miliyan 1.6 domin gudanar da shirin bayar da horo kan fasahar sola a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar da ke Yola.

Iliya ya bayyana cewa wadannan matakai suna cikin kokarin gwamnati na kara samar da lantarki da kuma amfani da sababbin fasahohi wajen ci gaban tattalin arzikin jihar.

Gwamnan jihar Adamawa
Gwamna Umaru Fintiri na jihar Adamawa. Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Source: Facebook

A wani bangare, kwamishinan lafiya, Felix Tangwami, tare da takwaransa na ilimi, Dr Umar Garba Pella, sun tabbatar da bullar cutar kwalara a yankunan Mubi ta Arewa da ta Kudu.

Sun ce an samu rahoton mutane 236 da suka kamu da cutar tare da rasa rayuka 13, inda suka shawarci jama’a da su kula sosai.

Bago ya dakatar da tura dalibai waje

Kara karanta wannan

Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Umaru Mohammed Bago ya halarci wani taro a jami'ar Abdulkadir Kure da ke jihar Neja.

Gwamna Bago ya yi alkawarin biya wa daliban da suka samu gurbin karatu kudin makaranta tare da musu kyauta ta musamman.

A taron, gwamnan ya sanar da dakatar da shirin tura dalibai 'yan asalin jihar karatu kasar waje tare da cewa za a yi amfani da kudin don inganta ilimi a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng