Dalilin Peter Obi na Zagaya Najeriya, Ya Na Ba Makarantu Kyautar Miliyoyin Naira
- Tsohon gwamna, Peter Obi, ya ce ya gina rayuwarsa a kan tallafawa ilimi da kiwon lafiya domin ɗaga martabar ɗan Adam
- 'Dan takarar shugaban kasar ya fadi hakan ne lokacin da ya ba da tallafin N15m ga kwalejin kiwon lafiya da ke Adazi Nnukwu
- A wani bangare na son ganin ci gaban kananan yara, Obi ya ce zai gina makarantar firamare da gobara ta kona a Anambra
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya yi maganar game da ayyukan jin kansa.
Peter Obi ya bayyana cewa manufarsa ta duniya ita ce gina rayuwar mutane ta hanyar tallafa wa harkokin ilimi da kiwon lafiya.

Source: Twitter
Peter Obi ya ba makaranta kyautar N15m

Kara karanta wannan
Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga
'Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da gudummawar Naira miliyan 15 ga kwalejin kiwon lafiya ta Adazi Nnukwu da ke Anaocha, in ji rahoton Tribune.
A yayin da yake ba da tallafin miliyoyin kudin, Peter Obi ya ce yana zagaya makarantu ne domin tallafa wa ɗalibai da ma’aikatan lafiya.
“Na yanke shawarar yin rayuwa mai cike da taimakon ɗan Adam. Ina zagaya Najeriya ina tallafawa makarantu saboda ilimi da lafiya sune ginshiƙai na rayuwa."
- Peter Obi.
Obi ya ƙara da cewa malaman jinya da likitoci sune ke gina rayuwa da kare lafiyar jama’a, saboda haka yake ba su tallafi a matsayin gudunmawar inganta al'umma.

Source: Twitter
Makarantar kiwon lafiya ta yaba wa Obi
Obi ya kuma yaba wa Bishof Paulinus Ezeokafor, shugaban cocin Katolika na Awka Diocese, wanda shi ne wanda ya kafa kwalejin.
Ya bayyana cewa tun lokacin da ya zama gwamna a 2006, babu makarantar kiwon lafiya ko ta ungozoma da aka amince da ita a jihar.
“Na nemi coci ta taimaka wajen samun izini da gyara makarantun kiwon lafiya. A yau wannan makaranta ta zama abin koyi,” in ji Obi.
Mrs. Okafor Chibugo, mukaddashiyar shugabar makarantar, ta bayyana cewa ziyarar Obi ta kara musu kwarin gwiwa don son ci gaba da ba da ilimin lafiya.
Obi zai gina makarantar da gobara ta kona
Daga nan Obi ya kai ziyara makarantar firamare da naziri ta Agulu Practicing, inda gobara ta kone gine-ginen makarantar a watan Disamba 2024.
Shugabar makarantar, Kwamared Eucharia Egwuonwu, ta bayyana cewa tun bayan gobarar ba a yi wani gyara ba, kuma dalibai suna karatu a cikin rana da ruwan sama.
Obi ya ce zai dauki nauyin sake gina makarantar daga watan Janairu 2026, domin ganin yara sun samu ingantaccen wurin karatu.
“Za mu fara aikin sake gina makarantar a watan Janairu domin yaran su koma karatu cikin jin daɗi.”
- In ji Peter Obi.
Kalli hotunan ziyarar Peter Obi zuwa kwalejin kiwon lafiyar, da ya wallafa a shafinsa na X a kasa.
Obi ya raba kudi a makarantun Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Peter Obi ya ba da kyautar N15m ga kwalejin jinya da makarantar islamiyya a Bauchi domin tallafa wa kiwon lafiya da ilimi.
Yayin da ya ce yana ziyartar akalla makarantun jinya 70 a shekara, Peter Obi ya ce malaman jinya su ne ginshikin dorewar rayuwar al'umma.
Shugabannin makarantun Malikiya da Intisharu sun gode wa Obi, tare da alkawarin amfani da kudin da ya ba su wajen inganta harkokin karatun makarantunsu.
Asali: Legit.ng

