Najeriya da Sauran Ƙasashen Afrika da Amurka Ke Yi Wa Kallon Barazana
Kalmar “Kasashen da ake musu kallon na musamman” (CPC) ta sake mamaye manyan labaran duniya, bayan wani sabon jawabi da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan zargin kisan kiyashin Kiristoci a Najeriya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaba Donald Trump ya bayyana kasar Najeriya da ke Afirka ta Yamma a matsayin kasa da ake zargn tana take hakkin addini.
Ana zargin jerin ƙasashen da aka saka a tsarin CPC da laifin takewa ko kuma sakaci wajen kare ‘yancin yin addini, bisa dokar yancin addini (IRFA) ta shekarar 1998 da aka yi wa gyaran fuska a 1999.

Source: Twitter
Wannan matsayi ya ba ministan harkokin wajen Amurka ikon tantance irin waɗannan ƙasashe, tare da bayar da shawarar matakan diflomasiyya ko takunkuman tattalin arziƙi domin rage zaluntar addini, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya
A kwanakin nan, lamarin ya dawo da hankalin duniya kan Najeriya bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ayyana ta a matsayin kasa da ake kallonta ta musamman, saboda zargin zaluntar Kiristoci a ƙasar.
Kasashen da Trump ya ke wa kallon barazana
Legit Hausa ta duba wasu kasashen Afirka da ke da matsala da Amurka musamman karkashin mulkin Donald Trump.
1. Kasar Najeriya
A kwanakin nan, Shugaba Donald Trump ya ayyana Najeriya a cikin kasashe da ake zargin suna take hakkin wani addini.
Zargin ya biyo bayan korafi daga al'ummar Kiristoci bayan wani Fasto daga jihar Benue ya bayyana halin da mabiya addinin suke ciki.
Daga bisani, Trump ya shawarci Najeriya da ta yi gaggawar daukar matakin kawo karshen yan ta'dda da masu tayar da kayar baya ko kuma ya dauki mataki.
Trump ya ce idan har gwamnatin Najeriya ba ta dauki mataki ba, ba shi da wani zabi illa daukar matakin soji kan kasar.
Najeriya ta fara shiga jerin kasashen da ke cikin CPC a shekarar 2020, a wa’adin farko na Donald Trump, amma daga baya gwamnatin Joe Biden ta cire ta daga jerin.
Sake sanya sunan Najeriyar yanzu ya biyo bayan matsin lamba daga ‘yan majalisar dokokin Amurka, ciki har da Ministan Harkokin Waje Marco Rubio, suna kira da a ɗauki ƙarin matakai kan batun ‘yancin yin addini.

Source: Getty Images
2. Kasar Eritrea
Eritrea ita ce kasa ta farko a Afirka da Amurka ta sanya ta jerin kasashen da ake zargin suna take hakkin gudanar da addini.
Tun daga shekarar 2004, aka sanya Eritrea cikin jerin ƙasashen CPC bisa dokar yancin addini ta kasa da kasa ta shekarar 1998, sashi na 402(b).
Shafin gwamnatin Amurka ya tabbatar da haka saboda zargin take hakkin yin addini ko kuma yarda da irin wannan take hakkin.
A ranar 29 ga Disamba, 2023, Ministan Harkokin Waje na Amurka ya sake sanya Eritrea cikin jerin ƙasashen CPC, tare da bayyana hukuncin takunkumin da ke tattare da wannan matsayi.
3. Kasar Afirka ta Kudu
Donald Trump ya sanar da cewa zai yanke dukan tallafin da yake ba kasar Afrika ta Kudu kan zargin kwace filayen wasu daidaiku a kasar.
Afirka ta Kudu ta mayar da martani inda ta ce kwace filayen da take yi yana daidai da doka kuma ta yi hakan ne domin kawo sauyi a kasar, cewar Reuters.
Har ila yau, Trump ya kakabawa kasar haraji a cikin tsarin sabon dokar kasuwanci da ya kawo wanda zai shafin tattalin arzikin Afrika ta Kudu.
Kasashe 5 da Trump ya gayyata Amurka
Sai dai a wani shiri na kulla yarjejeniya ta musamman kan inganta alaka da tattalin arziki, Trump ya gayyaci wasu kasashen Afirka biyar domin tattaunawa.
Kasashen sun hada da Senegal, Gabon, Guinea-Bissau, Liberia da kuma kasar Mauritania yayin da ya manta da sauran manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Nahiyar.
Rahoton BBC ya ce ganawar ta maida hankali ne kan manufar Trump ta “kasuwanci ba taimako ba”, kuma dukkansu na fuskantar tara kashi 10% kan kayayyakin da suke fitarwa zuwa Amurka.
Dalilin haka, ana ganin suna fatan cimma yarjejeniya domin rage wannan kaso na haraji kasa da sauran kasashen Nahiyar.

Source: Twitter
Barazanar Trump: EU ta goyi bayan Najeriya
Mun ba ku labarin cewa kungiyoyi da kasashen duniya da dama na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu bayan barazanar Amurka kan Najeriya.

Kara karanta wannan
'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Kungiyar Kasashen Turai ta bayyana matsayarta game da lamarin tare da kawo hanyoyin gyara dangantaka.
Jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot, ya ce kungiyar tana tare da Najeriya wajen yaki da tashin hankali da kare al'ummarta.
Asali: Legit.ng

