Gwamna Ya Dakatar da Sarkin da Ake Zargi Yana Daukar Nauyin Ta'addanci a Akwa Ibom
- Gwamnatin Akwa Ibom ta dakatar da Sarkin Ikot Umo Essien na tsawon watanni saboda zargin aikata ta’addanci
- Sarkin na fuskantar bincike kan zargin daukar nauyin 'yan ta'adda su tartwasa kasuwa da satar kayan gwamnati a garinsa
- Gwamnati ta kuma fayyace gaskiya game da zargin cewa ta janye jami’an tsaron tsohon gwamna Udom Emmanuel
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta dakatar da sarkin Ikot Umo Essien, da ke karamar hukumar Essien Udim.
Gwamna Umo Eno ya bada umarnin dakatar da basaraken ne bisa zarginsa da hannu a ayyukan ta’addanci da tayar da hankali a yankin.

Source: Twitter
An dakatar da sarki kan zargin ta'addanci
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu, Frank Archibong, ya fitar a garin Uyo ranar Laraba, in ji rahoton The Guardian.
Frank Archibong ya ce dakatarwar, wadda za ta ɗauki tsawon watanni shida, za ta bai wa gwamnati damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa sarkin.
Ya bayyana cewa ana zargin sarkin da daukar nauyin 'yan ta'adda su lalata sababbin gine-ginen kasuwar Ikot Ekpenyong, da kuma aikata ayyuka da ke kawo tashin hankali da rashin tsaro.
'Yan ta'adda sun lalata gine gine
Kwamishinan ya ce ’yan ta'adda daga Ikot Umo Essien sun kai hari kasuwar Ikot Ekpenyong, inda suka lalata sababbin shagunan da tsohon dan majalisar tarayya, Nsikak Ekong, ya dauki nauyi a Fabrairun 2024.
A cewarsa, maharan sun kuma rushe rijiyar burtsare ta shirin Fadama da bandakin jama’a, inda suka kwashe rufin aluminium, tagogi, ƙofofi, tankunan ruwa, famfo, da janareta.
Archibong ya ce waɗannan miyagun sun kuma tsoratar da mazauna yankin har ya je fa al'umma suka fara rayuwa cikin fargaba.
Ya kara da cewa binciken farko ya nuna cewa Chief Monday Esu, sarkin garin, na da hannu a lamarin, saboda haka aka umurce shi da ya mika duk wasu kayayyakin gwamnati da ke hannunsa ga sakataren majalisar masarautar garin.

Source: Facebook
Gwamnatin ta janye tsaron tsohon gwamna?
Tun kafin wannan, jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnatin Akwa Ibom ta karyata jita-jitar cewa an janye jami’an tsaron tsohon gwamna Udom Emmanuel, tana mai cewa labarin karya ne.
Kwamishinan yada labarai, Rt. Hon. Aniekan Umanah, ya bayyana cewa labarin “ƙarya ce da aka ƙirƙira don ruɗar da jama’a.”
Ya bayyana cewa umarnin janye jami’an tsaro yana karkashin Sufeto Janar na ƴan sanda (IGP) da kwamishinan ƴan sanda na jihar, ba gwamnati ba.
Kwamishinan ya kara da cewa dukkan tsofaffin gwamnoni a jihar na da hakkin samun jami’an tsaro, kuma babu wani rahoto da ya nuna an cire tsaron wani daga cikinsu.
An ba Tinubu sarauta a Akwa Ibom
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi sarautar gargajiya mafi girma a Akwa Ibom da ake kira "Otuekong."
Sarakunan gargajiya na jihar sun mika sarautar a fadar shugaban kasa tare da tawagar da Gwamna Umo Eno ya jagoranta.

Kara karanta wannan
Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja
Bayan karbar sarautar, Tinubu ya bayyana jin dadinsa da wannan karamci, yana mai tunawa da zamansa a Eket, a lokacin da yake aiki da kamfanin Mobil.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

