Majalisar Dattawa na So a Ajiye Motoci Masu Aiki da Fetur a Koma na Lantarki a Najeriya

Majalisar Dattawa na So a Ajiye Motoci Masu Aiki da Fetur a Koma na Lantarki a Najeriya

  • Majalisar Dattawa ta amince da dokar sauya motocin man fetur zuwa na wutar lantarki domin kare muhalli da haɓaka masana’antun cikin gida
  • Sanata Orji Kalu ne ya gabatar da kudirin, wanda ke neman kafa tsari domin samar da motocin wutar lantarki da samar da ayyuka masu yawa
  • Rahoto ya ce kudirin ya tanadi rangwamen biyan haraji da sauye-sauyen shigo da kaya, tare da wajabta kafa wuraren cajin mota a fadin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar dattawan Najeriya ta yi karatu na biyu ga kudirin da ke neman sauya motocin da ke amfani da man fetur zuwa motoci masu amfani da wutar lantarki.

Kudirin, wanda Sanata Orji Kalu ya gabatar, yana da nufin kafa tsarin da zai taimaka wajen samar da motocin wutar lantarki, ƙarfafa masana’antun cikin gida, da tabbatar da tsaftar muhalli.

Kara karanta wannan

A karshe, za a iya saka matatun man Najeriya a kasuwa domin sayar da su

Majalisar dattawa
Zauren majalisar dattawan Najeriya. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Yayin da ake tattaunawa a zauren majalisa ranar Laraba, Business Day ta ce Sanatocin sun jaddada cewa kudirin zai kawo sauyi ga harkar sufuri, makamashi da tattalin arzikin kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar kudirin da tasirinsa a Najeriya

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa manufar kudirin ita ce kawo sauyi daga dogaro da man fetur zuwa tsarin makamashi mai tsafta.

“Kudirin nan zai taimaka wajen rage hayakin da ke gurbata iska, da kuma tabbatar da cewa masana’antun cikin gida suna amfana da kasuwar motocin lantarki da ke tasowa a duniya,”

- Inji shi.

The Cable ta rahoto ya kara da cewa kudirin ya tanadi rangwamen haraji, cire harajin shigo da kaya ga masu kawo motocin lantarki.

Haka kuma, kudirin ya ce za a wajabta tashoshin mai a fadin kasa su samar da wuraren cajin motocin wutar lantarki.

Motocin lantarki za su karfafa Najeriya

Kudirin ya kuma bai wa Najeriya damar kare masana’antun cikin gida ta hanyar wajabta haɗin gwiwa tsakanin masu kera motoci na waje da kamfanonin cikin gida.

Kara karanta wannan

Satar mai: Majalisar dattawa ta bankado yadda aka wawure $300bn

Ya tanadi cewa duk wani kamfanin ƙera mota daga ƙasashen waje da ke aiki a Najeriya dole ne ya kafa masana’anta a cikin shekara uku a kasar.

Shugaban majalisar dattawa
Sanata Akpabio yana jawabi a majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Baya ga haka, daga shekarar 2030, kamfanonin za su rika amfani da aƙalla kashi 30 cikin 100 na kayan cikin gida Najeriya.

Wanda bai bi wannan sharadi ba zai fuskanci tarar Naira miliyan 250, yayin da marasa lasisi da ke shigo da motoci ba bisa ƙa’ida ba za su biya Naira miliyan 500 tare da kwace kayansu.

Sanatoci sun goyi bayan kudirin

Sanata Adamu Aliero ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta rage hayakin da ke cutar da lafiyar mutane a manyan birane kamar Legas da Kano.

“Motocin wutar lantarki za su taimaka wajen rage gurɓacewar iska da samar da ayyuka,”

Shi ma Sanata Osita Ngwu ya ce:

“Canjin yanayi na barazana ga al’ummomi, don haka wajibi ne mu rungumi wannan sabuwar fasaha.”

A nasa bangaren, Sanata Titus Zam ya yi gargadin cewa bai kamata Najeriya ta tsaya a gefe ba yayin da sauran kasashe ke cigaba da amfani da motocin wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta fara shirin tilasta koyarwa da harshen Hausa a makarantu

Majalisa za ta binciki ayyukan Buhari

A wani labarin, mun kawo muku cewa majalisar dattawa ta amince da bincike kan yadda aka yi ayyukan jiragen kasa a lokacin Muhammadu Buhari.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya bayyana cewa dole a binciki ayyukan lura da yadda jiragen kasa ke samun matsala sosai.

Majalisar ta ce ba zai yiwu a kashe makudan kudi wajen samar da jiragen ba kuma su fara lalacewa cikin kankanin lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng