Zargin Bai wa 'Yan Ta'adda Kudi: Gwamnatin Kaduna Ta Fadi Yadda Ta Taimaki 'Yan Bindiga
- Gwamnatin Kaduna ta bayyana yadda ta ke tallafa wa 'yan ta'adda da suka rungumi tsarin zaman lafiya tare da zubar da makamansu
- Karin bayaninta ya biyo bayan zargin tana raba kudi ga tsofaffin yan ta'adda a kokarinta na kawar da hare-haren 'yan bindiga a Kaduna
- Kwamishinan yada labaran jihar, Malam Ahmed Maiyaki ya ce sabon tsarin zaman lafiya a Kaduna ya maida hankali kan tattaunawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Kwamishinan yada labaran Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da tsarin biyan kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda.
Ya ce abin da maida hankali a kai shi ne samar masu da ilimi, kiwon lafiya, da daman neman abin yi domin kawo ƙarshen kisa da satar mutane a jihar.

Source: Facebook
Nigerian Trinune ta wallafa cewa Ahmed Maiyaki ya bayyana hakan ne yayin wani taron bita a kan yadda aikin jarida zai inganta zaman lafiya da ya gudana a jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kaduna na aiki da 'yan ta'adda
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Ahmed Maiyaki ya ce wannan sabon tsari da gwamnatin Kaduna ke amfani da shi yana haifar da saukin hare-hare.
Ya ce an bijiro da tsarin ne da nufin sauya salon amfani da musayar wuta zuwa tattaunawa, domin dawo da zaman lafiya a cikin al’umma.

Source: Original
A kalamansa:
“Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba, dole sai an samu fahimtar juna."
Kwamishinan ya ce an fara amfani da sabon salon ne a kan shugabannin ‘yan bindiga suka nemi gwamnati ta sake bude kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya da aka rufe saboda rashin tsaro.
Ya kara da cewa:
“Mun amince, domin wadannan bukatun ci gaban dan adam ne ba fansa ba. Ba mu ba su kobo ba , abin da mu ka yi shi ne dawo da abubuwan da jama'a ke amfani da su."

Kara karanta wannan
Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu
Zaman lafiya na dawowa a Kaduna
Ahmed Maiyaki ya bayyana cewa daga 2015 zuwa 2023, Kaduna ta fuskanci hare-hare da suka haura 1,160, inda aka kashe mutum 4,876 da kuma sace dubunnan mutane.
Duk da haka, ta hanyar hadin gwiwar Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da Kwamitin Zaman Lafiya na Kaduna, an kubutar da mutane sama da 500.
Maiyaki ya ambaci tsofaffin shugabannin ‘yan ta’adda irin su Jan Bros da Yellow One Million, wadanda yanzu ke taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.
Ya ce an dawo da fiye da hekta 500,000 na gonaki, kasuwanni sun bude, kuma yawon ‘yan kasuwa ya karu a yankunan da aka fi samun matsala, kamar Giwa, Birnin Gwari da Kauru.
Kwamishinan ya ce:
“Dukkanin makaranta ko asibiti da muka bude alamar nasara ce kan tsoro."
A bayaninta, Shugabar kungiyar 'yan jarida a Kaduna, Maryam Ahmadu-Suka, ta ce bitar ta koya wa manema labarai yadda za su yada labarai masu kawo sulhu maimakon tashin hankali.
Ana son yin sulhu da ƴan ta'adda
Kwamred Hamisu Sa'idu Batsari, shin ne shugaban ƙungiyar 'All for peace' ya shaida wa Legit cewa suna ganin sulhu ga yan yadda shi ne mafi alheri.
Ya bayyana cewa kungiyar da ya samar ce ta jagoranci yawancin zaman sulhun yan ta'adda da mazauna sassan Katsina.
Ya ce:
"Abin da ya da muka yi imanin cewa shi wannan hanyar na amfani da masalaha zai fi inganci wajen tabbatar da tsaro fiye da makami shi ne matsalar yanzu ana cikin shekaru sama da 10 ana fama."
"Kuma ana amfani da makami ne dabaru daban-daban, amma kwalliya ta ki ta biya kudin sabulu..
Kwamred Hamisu ya ce jama'a a kananan hukumomi daban-daban s Katsina sun fara cin amfani da sulhu wajen magance ta'addanci.
Kaduna: 'Yan ta'adda sun kai farmaki coci
A baya, mun wallafa cewa 'yan ta'adda sun sace mutum sama da 20 kuma sun hallaka wani malamin addini a ƙaramar hukumar Farin Dutse, Kauru, jihar Kaduna duk da kokarin gwamnati.
Harin ya faru da sanyin safiyar Talata, 28 Oktoba 2025, inda al’ummomi ke kira ga hukumomin tsaro da su hanzarta kawo karshen wannan al’amari da ke jawo asarar rayuka.
Shugaban cocin da aka kai harin, Fasto Amos Kiri, ya bayyana hakan kisan a matsayin rashin imani, inda ya ce sun dade suna fuskantar hare-hare a yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


