Trump: Najeriya Ta Gana da Jakadun Kasashe, an Yi Maganar Shari'ar Musulunci

Trump: Najeriya Ta Gana da Jakadun Kasashe, an Yi Maganar Shari'ar Musulunci

  • Gwamnatin tarayya ta gana da jakadun kasashe a Abuja don karyata zargin cewa ana kashe Kiristoci saboda addininsu
  • Ma’aikatar harkokin waje ta bayyana cewa dokokin ƙasa ba su nuna wariya ga kowa, kuma Shari’a tana aiki ne kawai ga Musulmi
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce barazanar Donald Trump ta samo asali ne daga rashin fahimta da aka samu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana ci gaba da tattaunawa da ƙasashen duniya don ƙarfafa haɗin kai da rundunonin tsaro.

Ana hakan ne domin shawo kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi da kuma zarge-zargen da ke cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta bayyana haka ne a wata ganawa da jakadun ƙasashen duniya da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanin sojoji a cikinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta ce Amurka ta yi kuskure

Rahoton Sahara Reporters ya ce ma’aikatar harkokin waje ta ce Amurka ta yi kuskuren sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna tauye ‘yancin addini.

Babban sakataren ma’aikatar, Dunoma Ahmed, ya ce wannan matsaya ta Amurka ta dogara ne da kuskuren fahimtar tsarin doka da zamantakewa na Najeriya.

Magana kan shari'ar Musulunci a Najeriya

Dunoma Ahmed ya bayyana cewa dokokin Najeriya ba su nuna bambanci tsakanin Musulmi da Kirista, kuma an tsara su ne don kare kowane ɓangare na al’umma.

Ya ce babu wata doka ta kasa da ke hukunci kan batanci ga addini, sai dai dokokin Shari’a da ake amfani da su a wasu jihohin Arewa da suka shafi Musulmi kawai.

Sakataren ya kara da cewa dokokin suna karkashin kulawar tsarin shari’ar ƙasa ce da doka ta tabbatar da su.

“Cibiyoyin Musulmai da Kiristoci suna aiki cikin ‘yanci, suna karfafa zaman lafiya da fahimtar juna,”

Kara karanta wannan

Majalisa za ta sa labule da gwamnatin tarayya kan barazanar Trump

- Inji shi

Ministan Tinubu ya karyata zargin Amurka

A nasa bangaren, ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Amurka ta yanke matsaya ne game da Najeriya a kan bayanan karya.

Mohammed Idris
Ministan yada labarai, Mohammed Idris. Hoto: Federal Ministry of Information
Source: Twitter

Ya ce matsalolin tsaro kamar ta’addanci, satar mutane da fashi ba su da alaƙa da addini:

“Ta’addanci da laifuffuka ba sa nuna bambancin addini. Wannan ba batun addini ba ne, batun laifi ne,”

Mohammed Idris ya bayyana cewa tun zuwan shugaba Bola Tinubu, jami’an tsaro sun kashe sama da ‘yan ta’adda 13,500, sun kama fiye da 17,000, sannan sun ceto mutum 9,850.

Ministan ya kara da cewa shugaban kasa na amfani da hanyoyin diflomasiyya don gyara kuskuren fahimta da gwamnatin Amurka ta nuna kan lamurran tsaron Najeriya.

Hafsan tsaro ya karyata ikirarin Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa hafsun tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa maganar ana kashe Kiristoci ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

"Najeriya ba ta da damar goyon bayan kisan addini": Minista ya karyata Trump a idon duniya

Janar Oluyede ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja bayan zargin da Amurka ta yi.

Ya kara da cewa rundunar sojin kasar na cigaba da kara kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda domin kawo zaman lafiya mai dorewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng