A Karshe, za a iya Saka Matatun Man Najeriya a Kasuwa domin Sayar da Su

A Karshe, za a iya Saka Matatun Man Najeriya a Kasuwa domin Sayar da Su

  • Gwamnatin Tarayya ta ce tana duba yiwuwar sayar da matatun man Warri, Fatakwal da Kaduna tare da fadin dalilan daukar matakin
  • Mai ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wani taro a kasar UAE
  • Ta ce cire tallafin mai ya buɗe sabon babi a kasuwar mai, inda gwamnati ke son masu fasaha da jari su shiga shirin sabunta matatun

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta ce ta buɗe kofa ga masu zuba jari da ke son sayen matatun mai na Warri, Fatakwal da Kaduna.

Jam'iar gwamnatin tarayya ta ce an yi haka ne domin sayar da matatun ya zama wani mataki na ƙara kuzari da gasa a harkar sarrafa mai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Trump: Najeriya ta gana da jakadun kasashe, an yi maganar Shari'ar Musulunci

Matatar Fatakwal
Matatar man Najeriya da ke Fatakwal. Hoto: NNPC Limited
Source: Twitter

Mai ba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan yayin wata hira da tashar Bloomberg.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yi bayanin ne a taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a birnin Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa.

Me yasa za a sayar da matatun Najeriya?

Verheijen ta bayyana cewa gwamnati na la’akari da yiwuwar sayar da matatun idan aka samu abokan haɗin gwiwa masu ƙwarewa da kuɗi da za su iya gudanar da ayyukan cikin nagarta.

Ta ce shirin yana ɗaya daga cikin matakan da gwamnati ke duba yiwuwar dauka domin tabbatar da inganci da tsari a ɓangaren mai na ƙasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Yarbawa ta fallasa shirin Trump kan Shugaba Tinubu

A cewarta:

“Wannan ɗaya ne daga cikin hanyoyin da za a iya bi idan aka samu abokin hulda da ya dace, tare da isasshen kudi.”

Ta kuma ƙara da cewa matatun sun dade suna aiki ne ƙarƙashin tsarin tallafi, wanda ya hana su yin gogayya da masana’antun mai masu zaman kansu.

Amfanin cire tallafin mai a Najeriya

Verheijen ta bayyana cewa cire tallafin man fetur ya kawo sauyi mai muhimmanci a kasuwar mai, inda yanzu kasuwar ta fara aiki bisa tsarin buƙata da gasa.

Daily Trust ta rahoto ta ce:

“Yanzu da muka cire tallafin, mun kawar da rudani a kasuwa,”

A cewar ta, wannan ne ya bai wa gwamnati damar jawo masu saka jari da za su taimaka wajen dawo da martabar matatun ƙasar.

Kara karanta wannan

Sakon Tinubu ga 'yan Najeriya a kan barazanar Donald Trump

Verheijen ta yaba wa shirin IPO na NNPCL

Verheijen ta ce gwamnati na kallon shirin fitar da hannun jarin NNPC (IPO) a matsayin matakin da zai ƙarfafa gaskiya da inganci a tsarin gudanarwar kamfanin.

Bayo Ojulari
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari. Hoto: NNPC Limited
Source: Twitter

Ta ce:

“Abu mafi muhimmanci ga masu ruwa da tsaki shi ne NNPCL ya zama mai gaskiya, mai inganci, da zai rika aiki yadda ya kamata.”

Shirin, a cewar ta, zai tabbatar da cewa NNPCL na tafiya da sababbin ka’idojin kasuwanci da ke bai wa kamfanin damar yin gogayya da sauran kamfanoni a duniya.

Dangote ya ki sayen matatun Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ba zai saye matatun man Najeriya ba.

Ya bayyana haka ne yayin da aka masa tambaya game da shirin fadada matatarsa zuwa mafi girma a duniya.

An bukaci ya saye matatun Najeriya maimakon fadada matatar shi, amma ya nuna hakan ba mai yiwuwa ba ne sam.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng