Zargin Triumph: Kungiyoyin Addinin Musulunci a Kano Sun Maka Gwamna Abba a gaban Kotu
- Wasu kungiyoyin musulmai 10 sun bayyana damuwarsa kan yadda ake tafiyar da batun zargin da ake yi wa Lawan Abubakar Triumph a Kano
- Tun a watan Satumba, 2025, wasu musulmai mabiya dariku suka zargi malamin musulunci da taba mutuncin Annabi Muhammad SAW
- Duk da matakin da gwamnatin Kano ta dauka domin gano gaskiya, kungiyoyi 10 sun kai karar Gwamna Abba da wasu mutum biyu kotu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wasu kungiyoyin musulmai akalla 10 sun shigar da ƙara a gaban kotu kan zargin batanci da ake yi wa Malam Lawan Abubakar Triumph.
Kungiyoyin sun bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf, kwamishinan 'yan sandan Kano, da Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na Kano a matsayin wadanda suke kara.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hakan na cikin wata takardar shigar kara a kotu da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan
Bayan daura aure, matashi 'dan shekara 25 ya caka wa matarsa wuka har lahira a Sakkwato
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan maka Gwamna Abba a kotu
Takardar kotun ta bayyana cewa kungiyoyin sun maka Gwamna Abba a kotu ne kan yadda ake tafiyar da zargin batanci ga Annabi SAW da ake ganin Sheikh Triumph ya yi a karatunsa.
Haka nan kuma takardar ta nuna cewa masu kara sun shigar da korafinsu ne a babbar kotun jihar Kano
Kungiyoyin sun zargi gwamnati da hukumomin tsaro da gaza aiwatar da aikinsu na doka wajen gurfanar da wanda ake zargi bisa kundin dokar Kano State Sharia Penal Code Law, 2000.
Sunayen kungiyoyin da suka kai kara
Masu ƙara sun haɗa da kungiyar Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, da Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative.
Sauran kungiyoyin su ne Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’tsa.
Daga cikin akwai gidauniyar Ashabul Kahfi Foundation da Majmau Ashabul Yameen, kamar yadda tashar Nasara Radio ta wallafa a Facebook.
An fara zargin Sheikh Triumph da rashin ladabi da munana kalamai ga Annabi Muhammadu SAW tun a watan Satumba, 2025.
Matakin da aka dauka kan zargin Triumph
Tun a lokacin, bayan wasu matasa sun yi zanga-zanga a kofar gidan gwamnatin jihar Kano, Gwamna Abba ya umarci Majalisar Shura ta Jiha da ta binciki lamarin.
Bayan nazarin faifan bidiyo da sauti, majalisar ta gayyaci Malam Triumph domin ya kare kansa, tare da kira ga jama’a da malaman addini da su guji yin kalaman da za su iya tayar da rikici.

Source: Facebook
Haka kuma, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta yi gargadi kan duk wani mataki ko magana da ka iya kawo tashin hankali, tana mai cewa za a bi doka da oda wajen gudanar da bincike.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Kano da Rundunar ‘Yan sanda ba su fitar da wata sanarwa kan ƙarar da kungiyoyin suka shigar ba tukuna.
Izala na goyon bayan Malam Triumph
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph.

Kara karanta wannan
'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Bala Lau ya bayyana cewa Ahlussunnah ne ke kare martabar Manzon Allah (S.A.W) tare da bin koyarwar Alƙur’ani da Hadisai.
Shugaban JIBWIS ya gargadi gwamnatin Kano da kada ta tsoma siyasa cikin binciken da ake yi kan muhawarar Triumph da wasu malamai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
