Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugabannin Al'umma 2 Yankar Rago a Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugabannin Al'umma 2 Yankar Rago a Jihar Katsina

  • Hare-haren yan bindiga na ci gaba da karuwa a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina duk da an yi sulhu
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sun shiga kauyen Doguwar Dorawa, sun kashe dattawa biyu da ake ganin girmansu
  • Mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa mutanen biyu yankar rago, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe shugabannin al'umma guda biyu a wani hari da suka kai Doguwar Ɗorawa, kusa da Guga a ƙaramar hukumar Bakori, jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a daren ranar Talata, inda aka kashe dattawa biyu masu fada-a ji a kauyen, Alhaji Bishir da ɗan uwansa, Alhaji Surajo.

Jihar Katsina.
Hoton taswirar jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta tattaro cewa yankar rago ‘yan bindigan suka yi wa mutanen biyu, ba harbinsu suka yi ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe mutum 2

Wani jigo a garin Guga, Mahadi Danbinta Guga, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata tattaunawa ta waya da manema labarai da safiyar ranar Laraba.

“Mun fuskanci mummunan hari jiya. Doguwar Ɗorawa ta rasa dattawa biyu da suke da girma a wurin al’umma. Suna cikin masu jagorantar jama’a don samar da zaman lafiya,” in ji shi.

Mahadi Guga ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, kuma sun ci karensu babu babbaka har tsawon awa ɗaya, ba tare da an kai dauki ba

Ya ƙara da cewa yana kan hanyarsa ta zuwa wajen jana’izar mamatan da kuma duba irin barnar da maharan suka yi.

Bayan kisan dattawan biyu, Mahadi ya ce yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da dama a lokacin harin.

Mazauna yankin sun yi zargin cewa yan bindigar mayakan Idi Abasu Aiki ko Kwashen Garuwa ne, wasu shugabannin daba da suka dade su na addabar yankunan Bakori da kewaye.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An lakadawa limamin masallacin Juma'a duka har ya mutu a Kwara

Hare-hare sun karu a yankin Bakori

Wani mazaunin yankun da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

"Da suka zo, sun ajiye baburansu a daji sannan suka kariso a ƙafa zuwa cikin gari domin aikata mummunan nufinsu.”

Mahadi Guga ya bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun zama ruwan dare a yankunan karamar hukumar Bakori duk da sulhu da ‘yan bindiga da aka yi.

Ya kara da cewa:

“Yanzu ba abin mamaki ba ne, kullum ana kai hari, duk da cewa gwamnati tana cewa ta yi sulhu da su."
Gwamna Dikko Radda.
Hoton gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.d
Source: Facebook

Har zuwa safiyar Laraba, babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Katsina ko ta ƙaramar hukumar Bakori kan lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wani jami'in rundunar yan sa-kai ta JTF a karamar hukumar Bakori ya shaida wa Legit Hausa cewa dama tun farko ba su goyon bayan wannan sulhun da aka yi da yan bindiga.

Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce idan aka duba tarihi, ba a taba sulhu da mutanen nan kuma suka rike amana ba.

Kara karanta wannan

Rubutu a Facebook ya jefa 'yan Kwankwasiyya 2 a gagarumar matsala a Kano

"Gwamnan Katsina da ya gabata ya yi sulhu da su, amma ka duba shekararsa ta karshe a kan mulki yadda hare-hare suka zama ruwan dare, shi yasa bana goyon bayan sulhu.
"Idan mutanen nan sun tuba, su tattaro makamansu su mika wa gwamnati, ita kuma ta taimaka masu ta yadda za su koma rayuwa kamar kowa, wanda kuma ba zai tuba ba, mu hadu a filin daga," in ji shi.

An kashe kasurgumin dan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa wani daga cikin hatsabiban ’yan bindiga ya rasa ransa yayin artabu da abokan gaba a jihar Katsina.

'Dan ta'addan da aka fi sani da Jankare ya rasa ransa a hannun wata dabar yan bindiga da suka yi musayar wuta.

Ana dai yawan samun arangama tsakanin yan bindiga da ke kai hare-hare saboda wasu dalilai na su na karan kansu a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262