Bukatu 19 da Likitoci Suka Gabatar wa Gwamnatin Tinubu kafin Janye Yajin Aiki

Bukatu 19 da Likitoci Suka Gabatar wa Gwamnatin Tinubu kafin Janye Yajin Aiki

  • Kungiyar likitocin NARD ta fara yajin aikin sai baba ta gani bayan karewar wa'adin kwanaki 30 da ta ba gwamnatin tarayya
  • Likitocin sun gabatar da bukatu 19 ga gwamnati ciki har da neman karin albashi, gyaran asibitoci, da inganta yanayin aiki
  • Shugaba Bola Tinubu dai ya umarci ministan lafiya ya gaggauta warware rikicin tare da tabbatar da komawar likitoci bakin aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD) ta fara yajin aikin sai baba ta gani na kasa baki ɗaya a ranar Asabar.

Tsumduma yajin aikin ya biyo bayan karewar wa’adin gargadin kwanaki 30 da kungiyar NARD ta bai wa gwamnatin tarayya.

Likitoci sun gabatar da bukatu 19 ga gwamnatin tarayya yayin da suka tsunduma yajin aiki
Hoton wata likita zaune cikin damuwa da hoton Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @Getty Images, @officialABAT/X
Source: Getty Images

Likitoci sun tsunduma yajin aiki

Shugaban ƙungiyar, Dr. Muhammad Suleiman, ya bayyana cewa yajin aikin ya zama dole sakamakon gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da ta sha yi, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Muhammad Suleiman ya ce:

“Mun yi haƙuri fiye da kima amma yanzu lokaci ya yi da za mu tsaya tsayin daka wajen neman hakkokinmu.”

A halin da ake ciki, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a da ta gaggauta warware rikicin tare da tabbatar da cewa likitocin sun koma bakin aiki cikin gaggawa.

Manyan bukatu 19 na likitoci ga gwamnati

Kungiyar NARD ta bayyana bukatu 19 da har yanzu gwamnati ta kasa cika su duk da tattaunawar da suka yi shi.

Ga jerin bukatun likitocin kamar haka:

  1. Rage ayyukan likitoci, wanda zai daidaita tsawon lokacin aiki domin kare lafiyar likitoci da marasa lafiya.
  2. Biyan ragowar karin albashin CONMESS (25% da 35%) daga watan Agusta 2025.
  3. Mayar da likitoci 5 da aka kora daga asibitin koyarwa na Lokoja tare da biyansu hakkokinsu.
  4. Biyan bashin karin girma da ya makale a asibitoci da dama.
  5. Biya kudin kaya da aka gaza sakinsu a 2024.
  6. Gyara matsalar jinkirin karin matsayi bayan kammala jarabawar zama kwararre.
  7. Biyan alawus din kwarewar aiki da likitocin suka shafe shekaru da dama suna bi.
  8. Shigar da jami'an lafiya na HO cikin tsarin aikin gwamnati tare da cikakken albashi da fa’idodi.
  9. Gyaran matsayin fara aikin gwamnati domin tabbatar da daidaiton matsayi da albashi.
  10. Ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar CBA da aka yi tun shekaru 16 da suka gabata.
  11. Gyaran kurakurai a alawus din kwararru da suka jawo aka samu ragin albashi.
  12. Daidaita matsayin likitoci na wucin-gadi da suka shafe shekaru ba tare da an ba su aiki na dindindin ba.
  13. Dakatar da rage darajar takardun WACP da WACS daga hukumar MDCN.
  14. Fitar da takardun kwarewa daga NPMCN ga waɗanda suka kammala karatu.
  15. Bai wa asibitoci 'yancin daukar ma’aikata ta hanyar tsarin maye gurbin wadanda suka bar aiki.
  16. Dakatar da hijirar likitoci zuwa kasashen waje (bisa dalilin labta masu aikin da a ake yi) ta hanyar inganta albashi da yanayin aiki.
  17. Inganta asibitoci da kayan aiki a duk fadin ƙasa.
  18. Dakatar da kirƙirar guraben aikin ba da shawarwari ga wadanda ba likitoci ba, saboda barazanarsa ga tsarin lafiya.
  19. Aiwatar da yarjejeniyar fansho na musamman da aka amince da ita tun Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Dalilin Peter Obi na zagaya Najeriya, ya na ba makarantu kyautar miliyoyin Naira

Likitoci sun ce ba za su janye yajin aiki ba har sai gwamnati ta biya bukatun da suka gabatar mata
Hoton wasu matasa sanye da kayan likitoci. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Gargadin likitoci ga gwamnatin tarayya

Dr. Suleiman ya jaddada cewa kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba har sai an cika dukkan bukatunsu.

Ya jaddada cewa:

“Ba mu da niyyar cutar da jama’a, amma rikon sakainar kashin gwamnati ne ya tilasta mu daukar wannan mataki.”

A halin yanzu, ma’aikatar lafiya tana ci gaba da tattaunawa tare da fatan cimma matsaya cikin mako guda.

"Ban ga laifin su ba" - Malama Safiyya

Wata ma'aikaciyar jinya da muka zanta da ita a jiha Kaduna, Malama Safiyya (wanda ba asalin sunanta ba ne) ta ce ba ta ga laifin likitocin da shiga yajin aiki ba.

Malama Safiyya ta ce:

"Gaskiya yana da kyau da suka tafi yajin aiki saboda likitoci da malaman jinya muhimman ma'aikatan lafiya ne, ya kamata a ce an biya bukatunsu sosai.
"Sun dade suna korafi, sun sha ba gwamnati wa'adi, duk dai ba a daidaita ba, yanzu da suka shiga yajin aikin ina ga za a sauraresu da kunnen basira.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fusata, ta dakatar da Musulmai kan 'shirin' kafa tsarin Musulunci a Jamus

"Ko da a ce ba a biya bukatunsu gaba daya ba, amma zai zama an duba muhimmai daga ciki an biya masu."

Malama Safiyya ta kuma ce bai kamata gwamnati ta yi watsi da bukatun likitoci da malaman jinya ba, la'akari da cewa babu wani fanni da gwamnatin ta biya ma bukatunsa.

Game da likitoci ko malaman jinya da ke tsallakewa suna neman aiki a kasashen waje, Malama Safiyya ta ce:

"Ba za ka iya tsayawa ka gina kasa ba idan kasa ba za ta gina ka ba. Idan an ba ka tallafi ka yi karatu, ka gode, amma ya kamata a duba yanayin aiki shi ma.
"Ya kamata a rika duba yanayin aikin su ma'aikatan lafiyar, domin sau tari kana aikin ne amma shi aikin ne yake so ya kwantar da kai kasa, ai ka ga ba dadi."

'Yan Najeriya na kukan tsadar jinya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yajin aikin likitocin NARD ya fara jefa mutane marasa lafiya cikin wahala musamman masu karamin karfi.

Rahoto ya nuna cewa mutane sun fara karkata zuwa asibitocin kudi domin samun kulawa amma suna kuka kan tsadar kudin jinya.

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanin sojoji a cikinsu

Kungiyar NARD ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025 kuma ta ce ba za ta janye ba sai an biya bukatunta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com