Trump Na Neman Kawo Hari, An Jibge Jami'an Tsaro 60000 domin Zaben Anambra
- Rundunar ‘yan sanda ta ce an tura jami’ai sama da 60,000 daga hukumomin tsaro don bada kariya yayin zaben gwamnan Anambra
- CP Abayomi Shogunle, wanda zai jagoranci hukumomin tsaro, ya ce an kafa cibiyar umarni ta musamman domin raba bayanan asiri
- Ya ce an haramta motsin manyan mutane da kuma kungiyoyin tsaro a rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamakon zaben jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - An tura jami’an tsaro fiye da 60,000 daga hukumomin tsaro daban-daban domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben gwamnan Anambra.
Kwamishinan ‘yan sanda da ke kula da zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a ranar Asabar, Abayomi Shogunle, ya bayyana hakan.

Source: Twitter
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Talata a Awka, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shogunle ya bayyana cewa an kafa cibiyar umarni guda wacce za ta ba da damar musayar bayanai cikin gaggawa da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.
Za a kafa rundunoni a kowace rumfar zabe
Kwamishinan ya ce kwamitin tsaro na zabe (ICCES) zai tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kare rumfunan zabe 5,720 a fadin jihar.
Haka kuma, an girke rundunonin tsaro a kan iyakokin kananan hukumomi da jihohi domin gaggauta mayar da martani idan an sami matsala.
An kuma bayyana cewa an aiwatar da tsarin IGP Kayode Egbetokun na yaki da laifuffukan zabe, wanda ya hada da hana satar akwati, sayen kuri’a, da tsoratar da masu kada kuri’a.
Bugu da kari, ofishin kula da laifuffukan zabe na rundunar ya fara sa ido a dandalin sada zumunta domin gano masu yada bayanan karya ko aikata laifuffukan yanar gizo da suka shafi zaben.
Ranar zabe: An gargadi manyan mutane
Shogunle ya sake jaddada cewa jami'an tsaron Agunechemba da sauran kungiyoyin tsaro na al’umma ba su da hurumin tsaro a lokacin zabe.
Jaridar Tribune ta rahoto Shogunle ya ce doka ta tanadi cewa hukumomin tsaro na tarayya kadai ne ke da ikon yin aikin tsaro yayin zaben jihohi.
Ya kuma gargadi manyan mutane da ke amfani da jami'an tsaron ba da kariya masu dauke da makamai da kada su kuskura su shiga rumfunan zabe, domin duk wanda aka kama za a cafke shi, a karbe makaman, sannan a gurfanar da shi a kotu.
Shogunle ya bayyana cewa ma’aikatan INEC, manema labarai da masu sa ido na kasa da kasa ne kawai za a bari su yi zirga-zirga cikin yankunan da aka ware domin aikin zabe.

Source: Original
’Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a
Kwamishinan ya roki ’yan siyasa, shugabannin al’umma da masu kada kuri’a da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro kafin, yayin, da bayan zaben jihar.
A cewar sanarwar, jama’a za su iya tuntubar kwamishinan kai tsaye ta lambar waya, 0809-600-0079 idan akwai matsalar tsaro ko korafi.
INEC ta sanya ranar zaben gwamnan Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
Shugaban INEC (na wancan lokaci), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja a taron tuntubar juna da jam’iyyun siyasa.
Farfesa Mahmood Yakubu ya ce jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da gwani daga 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu 2025 tare da yin bayani.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


