Majalisar Kano Ta Fara Shirin Tilasta Koyarwa da Harshen Hausa a Makarantu
- Majalisar dokokin jihar Kano ta fara duba kudurin doka da zai wajabta koyarwa da harshen mutum, musamman harshen Hausa
- Hon. Musa Ali Kachako ne ya dauki nauyin kudurin wanda ya ce zai taimaka wajen inganta fahimtar dalibai da rage faduwa a jarrabawa
- Kudurin ya shiga hannun Kwamitin Ilimi na majalisar dokokin domin karin nazari da bayar da shawarwari kafin karatun sa na gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki sabon mataki mai muhimmanci domin inganta harkar ilimi.
Ta dauki matakin ne ta hanyar gabatar da kudurin doka da zai tilasta amfani da harshen mutum, musamman harshen Hausa, a matsayin yaren koyarwa a dukkan makarantun jihar.

Source: Facebook
Tribune ta rahoto cewa dan majalisa mai wakiltar mazabar Takai, Hon. Musa Ali Kachako ne ya gabatar da kudirin.

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri zai tura dalibai 100 karatu kasar waje, zai kashe Naira Biliyan 2.7
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kachako ya ce kudurin a zauren majalisa yana mai cewa matakin ya yi kama da na kasashe kamar China, Japan da India da suka samu cigaba ta hanyar koyar da yara da yaren su na gida.
Amfanin koyarwa da harshen Hausa
'Dan majalisar ya ce amfani da harshen Hausa a matsayin yaren koyarwa zai taimaka wajen kara fahimtar darussa, rage yawan daliban da ke faduwa, da kuma hana guduwa a makaranta
Ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen kiyaye al’adun Hausawa da kara hada kan al’umma a cikin tsarin karatu.
A cewarsa:
“Wannan doka za ta kara darajar ilimi a jihar, ta kuma gina harsashin fahimta, musamman a fannonin kimiyya da fasaha domin saukaka wa dalibai.”
Kachako ya ce wannan kuduri zai zama ginshiki wajen tabbatar da cewa ilimi yana tafiya da ainihin harshen da dalibi ke fahimta tun daga tushe.
Majalisa ta tura kudurin zuwa kwamitin ilimi
Bayan tattaunawa a zauren majalisar, an tura kudurin zuwa ga Kwamitin Ilimi na dindindin domin yin karin bincike da bayar da shawarwari kan matakan aiwatarwa.
Shugaban majalisar ya ce ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahoto kafin karatun kudurin karo na biyu da na uku.

Source: Twitter
Wannan mataki, in ji shi, zai taimaka wajen tabbatar da cewa dokar da za a kafa ta dace da tsarin karatun zamani da bukatun jihar.
Shawarwari daga wasu 'yan majalisa
A wani bangare, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gabasawa, Hon. Zakariyya Abdullahi Nuhu, ya gabatar da kudiri na neman kafa Kwalejin Noma a mazabarsa.
Ya bayyana cewa kafa kwalejin zai taimaka wajen habaka ilimin noma da bunkasa tattalin arziki, ganin cewa sama da kashi 60 cikin 100 na mazauna mazabar su manoma ne.
The Nation ta rahoto ya ce:
“Kwalejin noma za ta ba da horo da dama ga matasa, ta kuma kara samar da ayyukan yi a yankin.”
Haka kuma, majalisar ta karanta wasika daga bangaren gwamnatin jihar wadda ke neman amincewa don kafa kwalejin fasaha a karamar hukumar Gaya.

Kara karanta wannan
Majalisar dattawa na so a ajiye motoci masu aiki da fetur a koma na lantarki a Najeriya
Legit ta tattauna da malamin makaranta
A tattauna wa da Legit Hausa, wani malamin makaranta a jihar Bauchi, Ibrahim Aminu Ilela ya ce akwai kalubale a dawowa amfani da harshen Hausa.
Ya ce:
"Abu ne mai kyau, ana so a samu hakan da dadewa. Sai dai idan aka yi dubi ga abubuwan da suka shafi kasa kamar aiki a majalisun kasa, zai zama koma baya ga wanda bai iya turanci ba.
"A Najeriya duk wanda bai iya turanci ba ana masa kallon maras ilimi ne, dole a fara kawar da matsalar nan a karon farko tukuna."
An yi zama kan tsaro a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zama da jami'an tsaro a jihar Kano.
An yi zaman ne bayan samun rahoto game da harin 'yan bindiga a wani yanki na jihar da ya jawo asarar rayuka.
Abba Kabir Yusuf ya bukaci shugabannin kananan huumomi su rika zama suna tattauna matsalar tsaro a Kano.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
