Tinubu Ya Tura Sunan Kwamishina Majalisa domin Tabbatar da Shi a Matsayin Minista
- Bayan murabus din ministan kimiyya da fasaha, Shugaba Bola Tinubu zai maye gurbinsa domin inganta gwamnatinsa
- Tinubu ya tura sunan babban lauya kuma kwamishinan Shari'a domin maye gurbin minista daga Enugu da ya ajiye aikinsa
- Geoffrey Uche Nnaji ya yi murabus ne bayan zarginsa da mika takardun bogi ga majalisa yayin da ake tantance shi kafin nada shi minista
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tura sunan wanda zai maye gurbin ministan kimiyya da fasaha da ya yi murabus.
Geoffrey Uche Nnaji ya yi murabus ne bayan zarginsa da mallakar takardun bogi wanda ya jawo maganganu a Najeriya.

Source: UGC
Rahoton TheCable ya ce Tinubu ya tura sunan Kingsley Tochukwu Udey domin tantance shi a matsayin minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ake yi wa tsohon minista, Nnaji
Hakan ya biyo bayan zargin tsohon ministan da mika takardun bogi ga Bola Tinubu da kuma majalisar tarayyar yayin tantance shi.
Uche Nnaji ya sha suka daga al'ummar Najeriya daban-daban kan zargin mallakar takardun bogi wanda ake ganin zubar da mutunci ne.
Daga bisani, bayan ce-ce-ku-ce, Nnaji ya hakura da muƙamin ministan inda ya rubuta takardar murabus wanda Shugaba Bola Tinubu ya amince da ita nan take.
Dalilin murabus din Nnaji daga kujerar minista
Bayanai sun fito kan dalilin murabus din tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji bayan zargin amfani da takardun bogi na digiri da na NYSC.
An ce wasu hadiman shugaban kasa sun bayyana cewa Bola Tinubu ne ya kira Nnaji zuwa fadar shugaban kasa, inda ya umurce shi da ya yi murabus.
Hakan ya biyo bayan wani bincike kan takardun ministan da aka ce ya gabatar da na bogi ga Bola Tinubu da kuma majalisar tarayya.

Source: Twitter
Minista: Tinubu ya tura sunan Udey majalisa
Shugaban kasar ya nemi majalisar dattawa ta amince da Udeh wanda babban lauya ne domin maye gurbin Geoffrey Uche Nnaji, cewar Punch.
Udeh shi ne babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Enugu a halin yanzu, wanda hakan ya nuna kwarewar sa a bangaren doka.
A cewar wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta, Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan aika sunan Udeh domin tabbatarwa.
Tinubu ya roki majalisar dattawa da ta duba bukatar cikin sauri, tare da bayyana godiya ga shugabannin majalisar bisa irin hadin kai da goyon baya.
Bayan karanta wasikar, Akpabio ya mika bukatar zuwa kwamitin majalisar gaba ɗaya domin fara nazarin gaggawa kan zababben ministan kasar.
Wadanda ake sa ran za su zama ministoci
Mun ba ku labari a baya cewa Ministan kimiyya da fasaha a Najeriya ya yi murabus saboda zargin gabatar da takardun bogi ga majalisar tarayya yayin tantance shi.
Murabus din Uche Nnaji, ya bude kofa ga nadin sabon minista daga Jihar Enugu, inda ake shirin fafatawa tsakanin tsofaffin gwamnoni biyu.
Masana siyasa sun ce Dr. Davidson Nnamani na da damar samun nasara, ganin shekarunsa da kwarewarsa a fannin dabarun tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

