An Yi Taron Habaka Noma da Rage Shigo da Kayan Abinci daga Waje zuwa Najeriya
- An bude zaman majalisar kasa kan noma da tsaron abinci domin nazari kan hanyoyin samar da abinci a Najeriya
- Babban sakataren ma’aikatar aikin gona ya ce taron zai taimaka wajen tsara dabarun rage dogaro da shigo da abinci
- Taron ya samu halartar wakilai daga jihohi, kungiyoyin kasa da kasa, da masu zuba jari a harkar noma a fadin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da zaman majalisar kasa na 47 kan aikin gona da tsaron abinci (NCAFS).
Rahotanni sun nuna cewa an shirya zaman ne domin cimma cikakken ikon samar da abinci da sauya fasalin noma a Najeriya.

Source: Twitter
Ma'aikatar yada labarai ta kasa ta wallafa a X cewa an gudanar da zaman ne a dakin taro na Musa Yar’Adua da ke Kaduna a ranar 3 ga Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana son rage shigo da abinci Najeriya
Babban sakataren ma’aikatar aikin gona da tsaron abinci na tarayya, Dr Marcus Ogunbiyi ne ya jagoranci bude zaman, inda ya ce taron zai taimaka wajen tsara manufofin da za su inganta noma.
Dr Ogunbiyi ya ce taken taron ya dace da manufar Renewed Hope ta shugaba Bola Tinubu wadda ke bai wa noma fifiko wajen farfado da tattalin arziki.
A bayanan da ya yi, ya ce ana duba bayanai da shawarwari daga jihohi, masu zuba jari da abokan hulɗa domin jagorantar sababbin manufofin kasa kan noma.
Ya ce manufar taron ita ce hada karfi da karfe tsakanin masana, manoma, da hukumomi domin fitar da dabaru da za su kara samar da abinci cikin gida da rage shigo da shi daga waje.
Kiran gwamnati ga masana noma
Babban sakataren ya bukaci mahalarta taron da su yi nazari kan abin da ya yi tasiri a baya, gano matsaloli, da tsara sabuwar hanya ga cigaban noma.

Source: Twitter
Ya kuma yaba da gudunmuwar abokan hulɗa kamar FAO, IFAD, WFP, AfDB, Bankin Duniya, USAID, da IFPRI, wadanda suka taimaka wajen inganta dabarun noma da tallafin fasaha.
Ogunbiyi ya bukaci mahalarta da su yi muhawarar cikin nutsuwa da hadin kai domin fitar da matakai masu amfani da za su karfafa Najeriya wajen samar da abinci.
Martanin gwamnatin jihar Kaduna
A jawabinsa na maraba, kwamishinan noma na Jihar Kaduna, Hon. Murtala Mohammad Dabo, ya ce jihar Kaduna da mutanenta sun yi farin cikin karbar wannan muhimmin taro.
Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a X cewa ya ce gwamnatin Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta dauki noma a matsayin tushen zaman lafiya da cigaba.
A yayin taron, an gabatar da takardu daga sassa daban-daban na ma’aikatar, ofisoshin jihohi, cibiyoyin bincike, da kungiyoyin kasa da kasa kamar ActionAid, GiZ, IFDC, da AGRA.
Ra'ayin 'yan Najeriya kan saukar farashi
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan saukar farashin abinci da aka samu a bana.
Masu sayayya sun ce saukin farashin ya sanya sun samu damar sayen kayan abinci masu yawa a kasuwa.
Wasu daga cikin 'yan Najeriya sun yi fatan Allah yasa saukar farashin kayan abinci ya dore domin cigaba da samun saukin rayuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


