Tinubu Ya Gwangwaje Tsohon Hafsan Sojoji da Ya Yi Ritaya, Ya Kara Masa Girma

Tinubu Ya Gwangwaje Tsohon Hafsan Sojoji da Ya Yi Ritaya, Ya Kara Masa Girma

  • Manjo Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim ya samu karin girma daga wajen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Karin girman ya zo masa ne a daidai lokacin da yake ritaya daga rundunar sojojin kasan Najeriya bayan ya kwashe shekaru yana hidimtawa kasa
  • Abdulsalam Bagudu ya taba rike mukamin mukaddashin babban hafsan sojojin kasa lokacin da mai rike da kujerar a wancan lokacin yake jinya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin girma ga Manjo Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim zuwa matsayin Laftanar Janar.

Shugaba Tinubu ya amince da karin girman ne yayin da yake barin aikin soja bayan shekaru masu yawa na yin hidima ga kasa.

Tinubu ya yi karin girma ga Manjo Janar Abdulsalam
Laftanar Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @HQNigerianArmy, @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Daily Nigerian ta ce kafin ritayarsa, Abdulsaman Bagudu Ibrahim ya kasance shugaban sashen manufofi da tsare-tsare a hedikwatar rundunar sojojin kasa.

Kara karanta wannan

Zargin kifar da Tinubu: Dan majalisa ya shiga kotu da rundunar sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya karawa Janar Abdulsalam girma

A mukamin da ya rike, ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara manyan dabarun tsaro da manufofin aiki da suka karfafa rundunar sojojin Najeriya.

A wani lokaci da tsohon babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya yi rashin lafiya, Manjo Janar Abdulsalam Ibrahim ne ya rike mukamin na wucin gadi.

Ya tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin rundunar sojojin cikin tsari har zuwa lokacin da shugaban kasa ya nada Laftanar Janar O.O. Oluyede a matsayin sabon babban hafsan sojojin kasa.

Amincewar shugaban kasa kan wannan karin girman ta biyo bayan irin misalin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa, lokacin da ya kara girma ga Laftanar Janar Lamidi Adeosun.

Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya taɓa zama shugaban sashen manufofi da tsare-tsare saboda kwarewa da jajircewarsa wajen hidimtawa kasa.

An yabawa matakin Shugaba Tinubu

Masu nazarin harkokin soja sun bayyana karin girma ga Abdulsalam Ibrahim a matsayin girmamawa mai cike da adalci, ga jami’i mai ladabi, basira, da kishin kasa, wanda ya yi fice wajen nuna gaskiya, kwarewa, da sadaukarwa a aikinsa.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin tsaro, an canjawa Janar sama da 60 wurin aiki

Tare da wannan karin girma, Laftanar Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim zai yi ritaya tare da cikakken gata da girmamawa da ake bai wa shugabannin rundunonin tsaro.

Manjo Janar Abdulsalam Bagudu ya samu karin girma
Manjo Janar Abdulsalam Bagudu wanda Tinubu ya karawa girma zuwa Laftanar Janar Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Karanta karin wasu labaran kan sojoji

Ribadu ya gana da hafsoshin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya kira taro na musamman da hafsoshin tsaro.

Nuhu Ribadu ya yi zaman ganawa da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri a babban birnin tarayya Abuja.

Ganawar ta su na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kawo farmaki a Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng