Shugaba Tinubu Ya Yi Nade Nade, Mutane 5 Sun Zama Manyan Sakatarorin Gwamnati

Shugaba Tinubu Ya Yi Nade Nade, Mutane 5 Sun Zama Manyan Sakatarorin Gwamnati

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori biyar domin cike guraben da ke ma’aikatar tarayya
  • Shugabar ma’aikatar tarayya, Didi Walson-Jack, ta ce an tantance wadanda aka nada cikin gaskiya da bin ƙa’idar aiki
  • Wadanda aka nada sun fito daga birnin Abuja, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabashin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori biyar domin cike guraben da ke cikin ma’aikatar tarayya.

Sanarwa ta fito ne daga bakin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, a wata takarda da jami'ar watsa labarai ta ma'aikatar, Mrs Eno Olotu, ta fitar a ranar Litinin a Abuja.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana zaune a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan wadanda aka nada ne a wani sako da tashar NTA ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Bayan PDP ta dare 2, kallo ya koma kan iko da hedkwatar jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, matakin na cikin tsarin gwamnatin Tinubu na tabbatar da cancanta, gaskiya da inganci a aikin gwamnati.

Sunayen sababbin manyan sakatarorin

Sababbin manyan sakatarorin da aka naɗa sun haɗa da Ibrahim Ozi daga babban birnin tarayya (Abuja), Ezemama Chidiebere daga jihar Imo.

Daga cikinsu akwai Garba Usman daga yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Ishiyaku daga Arewa maso Gabas, da Ukaire Chigbowu daga yankin Kudu maso Gabas.

Walson-Jack ta bayyana cewa an gudanar da tsarin tantancewa cikin tsanaki da gaskiya, domin tabbatar da cewa naɗin ya samu ne bisa cancanta, ba siyasa ko son rai ba.

Ta ce:

“Sababbin manyan sakatarorin suna da ƙwarewa da gogewa mai zurfi a fannoni daban-daban, abin da zai taimaka wajen ƙarfafa aikin gwamnati da inganta aiwatar da manufofin cigaban ƙasa.”

Muhimmancin naɗin ga cigaban ƙasa

Punch ta wallafa cewa shugabar ma’aikatar ta gode wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da gaskiya, cancanta da ƙwarewa a aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya dauki sabon salo, an dakatar da manyan shugabannin jam'iyyar

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ta ce waɗannan naɗe-naɗe sun nuna yadda gwamnatin Tinubu ke son ganin gwamnati mai sauraron bukatun ‘yan ƙasa da kuma samar da sakamako mai inganci.

A cewar ta:

“Gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar samar da kwararrun ma’aikata, domin tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun cimma nasara kamar yadda ake so.”

Dalilin cike guraben manyan sakatarorin

Rahotanni sun nuna cewa ofishin shugabar ma’aikatan tarayya ya fara aikin naɗa sababbin manyan sakatarori tun bayan amincewar shugaba Tinubu a ranar 15, Satumba, 2025.

Hakan ya biyo bayan kammala aikin wasu manyan sakatarori daga jihar Imo da birnin tarayya Abuja.

Baya ga haka, akwai buƙatar cike gurabe a yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas saboda ƙirƙirar sababbin ma’aikatu.

Sanusi II ya koka kan nade-naden Tinubu

A wani rahoton, mun labarta muku cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya koka kan yadda Bola Tinubu ya nada ministoci da dama.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin tsaro, an canjawa Janar sama da 60 wurin aiki

Ya ce hakan ba daidai ba ne idan har gwamnati na son rage kashe kudin gudanar da mulki bayan cire tallafin mai.

Khalifa Sanusi II ya ce ya kamata a yi amfani da kudin da aka samu bayan cire tallafi wajen ayyuka maimakon tara jami'an gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng