Kama Dalibin Jami'ar da Ya Soki Gwamna a Facebook Ya Fara Tayar da Kura a Jihar Neja

Kama Dalibin Jami'ar da Ya Soki Gwamna a Facebook Ya Fara Tayar da Kura a Jihar Neja

  • Kungiyar yan gwagwarmayar kare hakkin dan adam ta taso gwamnatin Neja da yan sanda kan kama dalibin IBBU, Abubakar Isah Mokwa
  • An kama dalibin jami'ar ne bisa zarginsa da cin mutuncin Gwamna Umaru Bago na jihar Neja a shafinsa na kafar sada zumunta
  • Kungiyar ta ce kama Abubakar ya nuna yunkurin hukumomin gwamnati na tauye hakkin fadar albarkacin baki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger - Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Hope Behind Bars Africa ta yi kira ga rundunar ‘yan sanda da ta gaggauta sakin Abubakar Isah Mokwa, ɗalibin jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kusan N5bn don wasu muhimman ayyuka

Kungiyar ta bukaci a saki dalibin, wanda yan sandan suka kama bisa zargin cin zarafin gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, a shafinsa na Facebook.

Gwamna Mohammed Umaru Bago.
Hoton mai girma Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago a gidan gwamnatinsa da ke Minna Hoto: @honbago
Source: Facebook

Premium Times ta tattaro cewa hakan na kushe ne a a wata sanarwa da Ogechi Ogwuma, jami’ar hulɗa da jama’a ta kungiyar, ta fitar ranar Litinin a Minna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce kamawa da tsare ɗalibin na Mokwa wani yunkuri ne na hana ‘yancin magana da tsoratar da matasa masu sukar gwamnati da kokarin fada mata gaskiya.

Dalilin kama dalibin jami'a a Neja

Rahotanni sun nuna cewa an kama Abubakar ne a ranar 23 ga Oktoba, 2025 kimanin mako guda bayan ya wallafa sakon sukar Gwamna Bago a shafinsa na Facebook.

Dalibin jami'ar ya yi zargin cewa gwamnan Bago yana “ƙarya game da nasarorin da gwamnatinsa ke ikirarin samu wajen yaƙi da rashin tsaro da gyaran tituna.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kama ɗalibin, yana mai cewa ana bincikensa bisa laifin cin zarafi ta intanet.

Kara karanta wannan

APC ta bankado shirin kai wa shugaban jam'iyya, Nentawe Yilwatda hari a Filato

Kungiya ta tsoma baki kan kama dalibi

Da take martani, Madam Ogwuma ta bayyana cewa:

“Wannan wata hujja ce da ke nuna yadda ake amfani da dokar yanar gizo don tsoratar da ‘yan kasa, musamman matasa masu ƙalubalantar masu mulki.
"Maimakon gwamnati ta yi tattaunawa da bin matakan gyara kan abin da aka faɗa, sai ta zabi ta yi amfani da doka don murƙushe ‘yancin faɗar albarkacin baki.”

Ta kuma jaddada cewa ‘yancin faɗar albarkacin baki haƙƙi ne da doka ta tabbatar da shi, ba wai alfarma ce daga gwamnati ba, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Gwamna Bago.
Hoton Gwamnan Naje, Mohammed Umaru Bago a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Minna Hoto: @Honbago
Source: Facebook

Kungiyar ta kuma bayyana cewa kama ɗalibi saboda sukar gwamnati ta yanar gizo abu ne da ya sabawa doka da ɗabi’a, tana mai cewa:

"Najeriya ba za ta ci gaba da kiran kanta ƙasa mai dimokuraɗiyya ba yayin da take tsare matasanta saboda faɗin gaskiya.”

Gwamna Bago ya taimaki dalibai 809

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umar Bago ya biya wa sababbin daliban da aka dauka a jami'ar Abdulkadir Kure da ke Minna kudin rijistar zangon karatu na 2024/2025.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Guinea Bissau bayan yunkurin juyin mulki

Daliban, wadanda suka haura mutum 800, za su yi karatu kyauta a zangon karatunsu na farko bisa umarnin Gwamna Bago.

Bayan haka, Gwamna Bago ya kuma sanar da soke shirin tura daliban jihar Neja zuwa karatu a kasashen ketare, yana mai cewa za a duba kudin don bunkasa ilimi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262