"Zan Goyi bayan Trump": Wike Ya Yi Magana kan Barazanar Trump
- Ana ci gaba da muhawara kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo farmakin soja a Najeriya
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi tsokaci kan matsalar ta'addanci a Najeriya da kalaman shugaban kasar Amurka
- Wike ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan duk masu son hadin gwiwa da Najeriya domin taimaka mata a yakin da take yi da ta'addanci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wa Najeriya.
Wike ya bayyana cewa a shirye yake ya nuna goyon baya ga Donald Trump, ko kowace kasa da ke da niyyar taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Politics Today na tashar Channels tv a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce yana maraba da duk wata irin haɗin gwiwar kasa da kasa da za ta karfafa yakin da Najeriya ke yi da ta’addanci.
Meyasa Wike zai goyi bayan Trump?
Ministan ya jaddada cewa irin wannan haɗakar ba bakon abu ba ne a tsakanin kasashe.
“Na ce zan goyi bayan Trump idan zai samar da tallafi da fasaha don taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci."
“Zan goyi bayan kowace kasa da ke son samar da mafita wajen tallafawa gwamnatin Najeriya a wannan fafutuka.”
- Nyesom Wike
Wike ya jaddada cewa ta’addanci matsala ce ta duniya da ke bukatar haɗin kai ba tare da la’akari da addini ko kasa ba.
“A karshe dai, kasashe da dama sun yi haka wajen yaki da ta’addanci. A wasu kasashe, wa ke tambaya ko mutum Musulmi ne ko Kirista ko mara imani? Ba wanda ke yin hakan.”
- Nyesom Wike

Source: Facebook
Trump ya yi wa Najeriya barazana

Kara karanta wannan
Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Furucinsa ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan kalaman Trump, wanda ya yi barazanar yiwuwar kawo hari na soja kan Najeriya bisa zargin wariya da cin zarafin Kiristoci a kasar.
Wike ya jaddada cewa abin da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne samar da haɗin gwiwar da za ta karfafa tsaron kasar, ba wai siyasantar da batun addini ko tsaron kasa ba.
Barazanar Trump: Hadimin Tinubu ya magantu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi tsokaci kan barazar da Shugaba Donald Trump, ya yi ta kawo hari Najeriya.
Daniel Bwala ya bayyana cewa zai zama babban kuskure ne idan Donald Trump ya dauki matakin soja kan Najeriya ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba.
Hadimin na Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakken ‘yancin gashin kai, kuma duk wani shiri na taimako kan harkokin tsaro dole ne ya kasance na haɗin gwiwa da kuma girmama ikon kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng