'Dan Majalisa a Amurka Ya Taɓo Kwankwaso kan Shari'a bayan Martani ga Trump

'Dan Majalisa a Amurka Ya Taɓo Kwankwaso kan Shari'a bayan Martani ga Trump

  • 'Dan majalisar Amurka Riley Moore ya dura kan Rabi'u Kwankwaso bayan ya yi martani ga barazanar Donald Trump
  • Moore ya zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da goyon bayan danniyar addini ta hanyar kafa dokar Shari’ar Musulunci
  • Kwankwaso ya ce Najeriya kasa ce mai yancin kai, yana kira ga hadin kan ‘yan kasa da tattaunawa maimakon barazana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Martanin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kan barazanar Amurka a Najeriya ya jawo magana.

An samu muhawara mai zafi a yanar gizo bayan dan majalisar wakilai na Amurka Riley M. Moore ya mayar da martani ga kalaman Sanata Rabiu Kwankwaso.

Dan majalisa a Amurka ya yi martani ga Kwankwaso
Dan majalisa, Riley Moore da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: RMKwankwaso/RepRileyMoore.
Source: Twitter

'Dan majalisar tarayya ya yi wannan martani ne a shafinsa na X a yammacin yau Litinin 3 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

"Zan goyi bayan Trump": Wike ya yi magana kan barazanar shugaban Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Kwankwaso kan barazanar Trump

Kwankwaso wanda ya taba zama tsohon gwamnan Kano, ya nuna damuwarsa kan kiran Trump na bayyana Nigeria a matsayin kasar da ake damuwa da ita kan batun addini.

A cikin sanarwar sa, Kwankwaso ya ce Trump bai kamata ya yi amfani da barazana ba, ya jaddada cewa Nigeria tana fama da kalubale daga kungiyoyin ta’addanci.

Ya kuma bukaci Amurka ta taimaka da fasahohin zamani wajen yaki da rashin tsaro maimakon tsoratarwa.

Kwankwaso ya kara jan hankali cewa a wannan lokaci, ‘yan Najeriya su mayar da hankali kan hadin kai da kare mutuncin kasa.

Kwankwaso ya ba Tinubu shawara kan barazanar Trump
Shugaba Bola Tinubu da Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abin da Moore ya ce ga Kwankwaso

Sai dai nan take, Moore ya mayar da martani mai zafi inda ya zargi Kwankwaso da nuna hali biyu, yana zargin sa da sanya dokar Shari’a a Kano lokacin yana gwamna.

Ya ce Kwankwaso ya rattaba hannu kan dokokin da ke hukunta masu batanci da kisa, kuma hakan ya sabawa ‘yancin addini da Amurka ke karewa.

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Ya ce:

"Gwamna - ko za ka iya yin martani kan gudunmawar da ka bayar kan kisan Kiristoci? Ka sanya hannu a dokar da ta tilasta kashe wanda suka yi batanci."

Wannan martani ya kara hura wutar tattaunawa game da ‘yancin addini a Nigeria, musamman a yankunan Arewa inda Shari’a take aiki.

Zuwa yanzu dai Rabiu Kwankwaso bai maidawa 'dan siyasar Amurkan da amsa ba.

Masu lura da harkokin siyasa sun ce wannan takaddama tana iya kara tsananta dangantaka tsakanin kasashen biyu idan ba a bi ta hanyar diplomasiyya ba.

Har ila yau, daukacin al’umma da masu fashin baki na ci gaba da bibiyar abin da zai biyo baya, domin Donald Trump ya ce ana cin zarafin Kiristoci a Nigeria.

A gefe guda kuma, wasu ‘yan Najeriya na ganin irin wadannan kalamai na iya kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kai a cikin kasa.

Kasashen duniya na ci gaba da sa ido kan yadda wannan lamarin zai kare, domin batun kare ‘yancin addini da martabar kasa ya kasance babban jigo mai tayar da hankali.

Kara karanta wannan

"Abin da dole Trump ya yi kafin kawo hari Najeriya": Hadimin Tinubu ya yi bayani

Ribadu ya sanya labule hafsoshin tsaro

Mun ba ku labarin cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya kira manyan hafsoshin tsaro domin ganawa da su.

Ribadu ya shiga ganawa da hafsoshin tsaron tare da wasu shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri a birnin Abuja.

Ganawar tasu dai na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar daukar matakin soja kan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.