Kiristoci: Peter Obi Ya Fadi Matsayarsa kan Yunkurin Amurka na Kawo Farmaki Najeriya
- Peter Obi ya nuna damuwa kan sanya Najeriya a jerin kasashen da ake da matsalar yancin addini da yunkurin Amurka na turo sojojinta
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce Najeriya na fama da matsalar tsaro mai munin da ba a taba gani ba a tarihi
- Duk da haka ya bukaci gwamnatin Najeriya da Amurka su zauna su fahimci juna, su hada kai wajen dawo da zaman lafiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana matsayarsa kan zargin kisan kiristoci a Najeriya.
Obi ya nuna damuwa kan matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu “Babbar Matsala kan Yancin Addini."

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra ya wallafa a shafinsa na X yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsayar Peter Obi kan barazanar Amurka
Mista Peter Obi ya kuma nuna damuwarsa kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na yiwuwar kawo hari ta sama da kasa a wasu yankunan Najeriya.
Obi ya ce wannan matsaya ta Amurka ta kai ta tayar wa duk mai kishin ƙasa hankali, duba da yadda matsalar tsaro ke taɓarɓarewa fiye da kowane lokaci a tarihin Najeriya.
"Babu shakka, Najeriya tana fuskantar matsalar tsaro da ba ta taɓa ganin kamarta ba, inda ake rasa rayuka da dukiyoyi gunin ban mamaki.
“Rahoton kungiyar Amnesty International ya nuna cewa sama da mutane 10,000 ne aka kashe tun watan Mayu 2023.
"Wannan kisan da ake yi wa ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba abin Allah wadai ne, kuma dole ne a ɗauki dukkan matakai don kawo ƙarshensa.”
- Peter Obi.
Obi ya bukaci samun shugabanci nagari
Mista Obi ya kuma jaddada cewa matsalar tsaro da ƙasar ke ciki na iya zama tarihi idan aka samu jagoranci nagari da gwamnati mai ƙwazo.
“Duk da ba a wannan gwamnatin aka fara wannan matsala ba, amma abin takaicin shi ne gazawar shugabannin APC wajen nuna ƙwarewa, kishin ƙasa da rike amanar dukiyar kasa.
“Sun kasa jagorantar ƙasar ta yadda babu wanda za a zalunta ko kashe shi ba bisa ka’ida ba, a samu ƙasa mai zaman lafiya, gaskiya da adalci.”

Source: Twitter
Mafitar da Peter Obi ya kawo
Tsohon gwamnan ya nanata cewa Najeriya da Amurka ƙasashe ne masu bin tsarin dimokuraɗiyya, kuma suna da alaka mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Bisa haka, Obi ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta Amurka su zauna su tattauna don fahimtar juna tare da aiki tare wajen magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.
Ya ce lokaci ya yi da Najeriya da Amurka za su yi aiki tare cikin gaggawa domin dawo da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
Bwala ya yi bayani kan barazanar Trump
A wani labarin, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce Amurka ba za ta kawo hari Najeriya ba sai da amincewar gwamnatin tarayya.
Daniel Bwala ya ce sabawa diflomasiyya ne idan Amurka ta aiwatar wani matakin soja a Najeriya ba tare da neman izini daga gwamnati ba.
Bwala ya yi watsi da zargin cewa ana gudanar da kisan gilla kan Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa rashin tsaro na shafar ‘yan kasa ne gaba ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


