Martanin Wasu Manyan Arewa kan Barazanar Trump Ta kai Farmaki Najeriya
Mun hada muku rahoto na musamman a kan martanin da wasu 'yan Arewa suka yi game da barazanar Donald Trump ga Najeriya kan zargin kisan Kiristoci.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce ne shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Bayan martanin fadar shugaban kasa, Donald Trump ya yi barazanar kai hari Najeriya domin kare Kiristoci daga hare-hare.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun kawo muku maganganun da wasu 'yan Arewa da suka hada da Rabiu Musa Kwankwaso suka yi kan zargin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Martanin Rabiu Kwankwaso ga Trump
A sakon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce ya lura da karuwar maganganun da shugaban Amurka, Donald Trump, ke yi game da Najeriya.
Kwankwaso ya jaddada cewa Najeriya kasa ce mai cikakken ‘yancin kai, wadda jama’arta ke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda da miyagu daga sassa daban-daban.
Ya kara da cewa matsalar tsaro da ake fama da ita ba ta bambanta tsakanin addini, kabila ko ra’ayin siyasa.

Source: Facebook
A cewarsa, kamata ya yi kasashen Amurka su taimaka wa hukumomin Najeriya da fasahohin zamani domin magance wadannan matsaloli, maimakon yin barazana.
2. Kiran Sule Lamido ga Tinubu
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce barazanar Donald Trump ta kai harin soji Najeriya bisa zargin kisan kare dangi tana da hatsari ga kasar.
A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, Sule Lamido ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kira taron gaggawa da dukkan tsofaffin shugabannin kasar.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Sule Lamido ya bukaci a yi taron ne domin tattaunawa da samo mafita kan barazanar da Amurka ke yi wa Najeriya.
Sule Lamido ya jaddada cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su hadu wuri guda wajen kare ikon kasarsu domin kauce wa abin da ya bayyana a matsayin “barazanar da ke kara kusantowa.”

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita
3. Sheikh Gumi ya nemi a rabu da Amurka
Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi Allah wadai da barazanar da Trump ya yi wa Najeriya.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Malamin ya ce:
"Barazanar Trump ta kai harin soji kan ƙasa mai ‘yancin kai rashin girmamawa ne ga ikonmu."

Source: Facebook
"Shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka; ko su janye barazanar, ko mu katse dangantakar diplomasiyya da wannan gwamnatin."
Sheikh Gumi ya ce idan Najeriya ta yanke alaka da Amurka, akwai wasu hanyoyin fadada tattalin arziki da ƙarfafa kawancen soja.
4. Buratai ya yi kira ga shugaba Trump
Tsohon hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi kira da a yi taka tsantsan kan halin da ake ciki tsakanin Najeriya da Amurka.
Janar Buratai ya bayyana yaɗuwar labari maras tushe a matsayin muhimmin abin da ke haifar da rashin fahimta tsakanin kasashen biyu.

Source: Facebook
Rahoton VON ya nuna cewa ya jaddada bukatar a wuce matakin yaɗa bayanan karya domin ƙarfafa dangantakar diplomasiyya da kuma gina amincewa tsakanin Najeriya da Amurka.

Kara karanta wannan
Sule Lamido ya shawarci Tinubu ya tattaro tsofaffin shugabannin kasa kan barazanar Trump
Janar Buratai ya kuma shawarci Amurka da ta sauya matsayinta daga matsin lamba a zuwa haɗin kai da Najeriya.
5. Shehu Sani ya karyata ikirarin Trump
Sanata Shehu Sani ya ce ya fahimci cewa Najeriya na daga cikin kasashe 12 Amurka ta sanya cikin jerin kasashen da za ta mayar da hankali a kansu.
Ya ce matakin da aka dauka a kan Najeriya ya ta’allaka ne saboda ƙarya da kuma yaɗa bayanan da ba su da tushe.
Sanatan ya kara da cewa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a Najeriya suna kisa da garkuwa da mutane ba tare da la’akari da addininsu ba.

Source: Facebook
Shehu Sani ya wallafa a X cewa idan aka duba yawan Musulmai da Kiristoci a Najeriya, kusan ba zai yiwu wani addini ta zalunci wani ba kamar yadda ake fada.
Ya kara da cewa Trump ya samu bayanan da ba su da tushe daga ‘yan tayar da zaune tsaye da ke neman amfana daga rikici da rarrabuwar kawuna.
Zakzaki ya yi wa Trump martani
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar IMN ta 'yan Shia'a, Ibrahim Zakzaky ya yi Allah wadai da kalaman Trump game da Najeriya.
Malam Zakzaky ya ce zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba gaskiya ba ne kwata-kwata.
Ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da zargin tare da cigaba da hada kai da juna domin magance matsalolin tsaro a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

