Tsohon Hafsan Sojoji Ya Gargadi Trump bayan Barazanar Kawo Hari Najeriya, Buratai Ya Bada Mafita

Tsohon Hafsan Sojoji Ya Gargadi Trump bayan Barazanar Kawo Hari Najeriya, Buratai Ya Bada Mafita

  • Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya gargadi Amurka da ta guji barazana ga Najeriya
  • Ya bayyana cewa wannan barazana da Amurka ta yi ba zai haifar da 'da mai ido ba, illa dai a bi ta hanyar lalama da diflomasiyya
  • Janar Tukur Buratai ya soki ikirarin cewa ana yiwa kiristoci kisan kare dangi, lamarin da ya ce babu kamshin gaskiya a cikinsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon shugaban rundunar soji, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya shawarci gwamnatin Amurka da ta janye barazana ga Najeriya.

Ya bayyana cewa abin da zai kawo sauki shi ne kasar ta rungumi hanyar hadin kai maimakon amfani da karfi a dangantakarta da Najeriya.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya shawarci Tinubu ya tattaro tsofaffin shugabannin kasa kan barazanar Trump

Buratai ya shawarci Trump ya lallaba Najeriya
Shugaban Amurka, Donald Trump da Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya Hoto: Donald J Trump/Tukur Buratai
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Buratai ya bayyana cewa ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya “karya ce mai hatsarin gaske.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tukur Buratai ya caccaki Donald Trump

Sanarwar ta kara da cewa batyun da Trump ya yi na iya haddasa mummunan tasiri ga tsaron yankin Afrika ta Yamma.

A kalamansa:

“Labarin kisan Kiristoci wani salo ne mai sarkakiya gaskiya, kuma yana da matukar rikitarwa a Najeriya. Idan Amurka ta dauki wannan magana da muhimmanci, hakan zai zama babban kuskuren dabarun tsaro."
Buratai ya caccaki kalaman Trump a kan Najeriya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trumo
Source: Getty Images

Ya ce barazanar da gwamnatin Amurka ke yi, ciki har da batun tura sojoji zuwa Najeriya na iya jefa kasar cikin rikici.

Ya kara da cewa hakan zai iya hade al’ummar Najeriya gaba daya wajen ganin Amurka a matsayin mai neman mamaya.

Tukur Buratai ya shawarci Amurka

Buratai ya bayyana cewa Amurka za ta fi cin gajiyar inganta hadin gwiwar tsaro, kamar bayar da taimakon bayanan leken asiri da koyar da dabarun yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

'Kamar Libya, Iraq,' Sowore ya fadi hadarin zuwan sojojin Amurka Najeriya

Ya ce haka kuma Amurka za ta ci moriyar bayar da kayan aiki don magance matsalolin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da tsakiyar Najeriya.

Buratai ya kara da cewa:

“Amurka za ta yi babban kuskure idan ta dauki hanya ta tilastawa Najeriya. Kasar mu ce mafi yawan jama’a a Afrika kuma mafi karfin tattalin arziki. Amfani da barazana zai rage mutuncin Amurka."

Tsohon hafsan tsaron ya kara da cewa idan Amurka ta ci gaba da matsin lamba, hakan zai tilasta Najeriya da kasashen ECOWAS su kara kusanci da Rasha da China.

Sule Lamido ya shawarci Tinubu kan Amurka

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hado kawunan tsofaffin shugabannin Najeriya kan ikirarin Donald Trump.

Sule Lamido ya ce irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samo mafita ta diflomasiyya, saboda tsofaffin shugabannin na da sani a kan harkokin mu'amala da kasashen waje.

Ya ƙara da cewa barazanar Donald Trump na kawo hari kasar nan za ta jefa Najeriya cikin yanayi mai haɗari, zai kuma ƙara haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng