Sule Lamido Ya Shawarci Tinubu Ya Tattaro Tsofaffin Shugabannin Kasa kan Barazanar Trump
- Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya nuna damuwa kan barazanar yaki da ake zargin Shugaba Donald Trump ya yi wa Najeriya
- Sule Lamido ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kira taron sirri da tsofaffin shugabannin kasa don kare martabar kasar nan daga 'yan kasar waje
- Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a hada kai wajen tabbatar da kare 'yancin Najeriya domin kare barkewar hatsaniya a kasar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana damuwarsa matuka kan barazanar Donald Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa Najeriya barazanar kutse tare da kawo mata hari, yana cewa hakan batu na da hadarin gaske.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita

Source: Facebook
The Guardian ta wallafa cewa Sule Lamido ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar bayan Trumo ya waiwayo Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya shawarci 'yan Najeriya
Daily Post ta wallafa cewa Sule Lamido ya kira ‘yan Najeriya da su hada kai don kare martabar kasa, yana mai jaddada cewa lokaci ne da ake bukatar hadin kan kasa, ba rarrabuwar kawuna ba.
Ya kara da cewa:
“Barazanar yaki da Shugaba Trump ya yi wa Najeriya, lamari ne mai tayar da hankali."

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Jigawa ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da ya kamata kasar nan ta dunkule duk da kokarin cusa tsoro da barazana a zukatan 'yan Najeriya.
Sule Lamido ya shawarci Tinubu
Sule Lamido ya bayyana cewa tsofaffin shugabanni suna da kwarewar diflomasiyya da damar shiga tattaunawa kai tsaye da gwamnatin Amurka wajen rage zafin wannan barazana.
Ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bar girman kai, ya kira taron sirri da duk tsofaffin shugabannin kasa domin tattaunawa kan wannan barazana.
A kalamansa:
“Dole ne Tinubu ya danne girman kai, ya gayyaci duk tsofaffin shugabanni don su tattauna a sirrance, su nemo mafita a kan wannan mummunan lamari."
Ya kara da cewa wannan hanya ce da za a bi wajen saukaka matsalolin da kasar nan ke fuskanta na rashin tsaro a sassadaban-daban.
Sule Lamido ya kara da cewa wannan mataki zai kuma baiwa kasar nan dama na iya dakile barazanar da Donald Trump ya yi kafin lamarin ya yi kamari.
Sanata Kwankwaso ya shawarci Donald Trump
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da rashin tsaro maimakon yin barazana da yaki.
Sanata Kwankwaso ya ce barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ba ta dace da tsarin diflomasiyya ba, domin matsalar tsaro a Najeriya ba ta da alaka da addini ko kabila a Najeriya.
Ya kuma shawarci gwamnatin Tarayya da ta nada jakadu na musamman da za su yi aiki kai tsaye da gwamnatin Amurka wajen kare muradun Najeriya a matakin kasa da kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

