Abba Ya Fadi Yankuna 5 a Kano da za Su Iya Fin Samun Barazanar 'Yan Bindiga
- Gwamnan Kano ya ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a yankunan kan iyaka bayan harin ‘yan bindiga da ya kashe mutane
- Ya umurci shugabannin kananan hukumomi su gudanar da tarurrukan tsaro tare da jami’an tsaro da sarakuna a yankunan
- Abba Kabir ya ce tsaro shi ne abin da gwamnatinsa ta fi dauka da muhimmanci kuma ya jajanta wa iyalan da abin ya shafa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin tsaurara tsaro a kan iyakokin jihar, sakamakon harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane uku a Shanono da Tsanyawa.
Ya ce dole ne a tashi tsaye wajen hada karfi da karfe tsakanin hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin kare rayuka da dukiyar jama’a.

Source: Facebook
Tribune ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, bayan taron majalisar tsaro ta jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon Abba ga kananan hukumomin Kano
A cikin umarnin nasa, Abba Kabir ya ba da shawarar cewa dukkan shugabannin kananan hukumomi su riƙa gudanar da tarurrukan tsaro a kai a kai tare da jami’an tsaro da sarakuna.
A cewarsa:
“Hadin kai a matakin ƙasa shi ne mabuɗin dakile hare-haren ‘yan ta’adda da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a.”
Gwamnan ya ce wannan tsarin zai taimaka wajen samar da bayanan leƙen asiri daga jama'a, domin a iya gano barazanar 'yan ta'adda kafin kai hari.
Yankunan Kano 5 da ke bukatar kulawa
A yayin taron, gwamnan ya bayyana wasu kananan hukumomi biyar da ke bukatar kulawa ta musamman, ciki har da Shanono, Tsanyawa, Tudun Wada, Doguwa da Gwarzo.
Ya ce wadannan yankuna suna da muhimmanci ga cigaban tsaro a jihar saboda kusancinsu da jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da tsaro da zaman lafiya a dukkan fadin jihar.
Bugu da kari, jaridar Business Day ta wallafa cewa mutanen yankunan sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki.
Yadda aka yi taro kan tsaro a Kano
Taron majalisar tsaron ya samu halartar manyan kwamandojin rundunar sojojin Najeriya, rundunar sojin sama da ta ruwa, kwamishinan ‘yan sanda, kwamandan NSCDC.
Haka zalika, taron ya samu halartar shugabannin hukumomi irin su NDLEA, NAPTIP, ICPC, da FRSC.

Source: Facebook
Baya ga haka, shugabannin hukumar shige da fice, kwastam, da gidajen gyaran hali sun halarci taron, tare da shugabannin kananan hukumomi.
Gwamnan ya yaba da irin jajircewar hukumomin tsaro da sauran shugabanni wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Abba Kabir ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin, tare da tabbatar da cewa gwamnati ba za ta bar lamarin haka nan ba.
An sace dan majalisar jihar Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sace mataimakin shugaban majalisar jihar Kebbi, Hon. Muhammad Sama'ila Bagudu.

Kara karanta wannan
Trump ya sa Najeriya a jan layi kan zargin kashe Kiristoci, Amurka za ta yi bincike
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa an sace Hon. Bagudu ne jim kadan bayan fitowa daga masallaci zai tafi gida.
Bayan sanar da yadda aka sace shi, kakakin 'yan sandan jihar ya bayyana cewa sun dukufa wajen ceto dan majalisar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
