Abin da Ake Nufi idan Amurka Ta Sanya Kasa cikin Jerin Kasashe Masu Babbar Matsala
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kira 'masu babbar matsala' watan (CPC).
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Sanya kasa a CPC na nufin ta shiga cikin kasashen da ke take ’yancin gudanar da addini.

Source: Twitter
Trump ya dauki mataki kan Najeriya
Shugaba Trump ya sanar da sanya Najeriya cikin CPC ne ranar Jumma’a, 31 ga watan Oktoban 2025 a wani rubutu a shafinsa na Truth Social wanda aka yada a shafin White House na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya dauki matakin ne a matsayin martani ga zarge-zargen kisan gilla ga Kiristoci da ake cewa yana gudana a Najeriya.
"Kiristanci yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci. Masu tsatstsauran ra'ayin Islama ke da alhaki kan wannan kisan. Saboda haka na sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu babbar matsala."
"Amurka ba za ta tsaya gefe tana kallo ba yayin da irin waɗannan mummunan laifuffuka ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe. Za mu dauki mataki don kare Kiristoci a duniya.”
Trump ya taba sa Najeriya cikin CPC
Jaridar The Cable ta ce ba wannan ne karo na farko da Trump ya ɗauki irin wannan mataki ba.
A ƙarshen wa’adin mulkinsa na farko a 2020, Najeriya ta shiga jerin CPC, kafin gwamnatin Joe Biden ta cire sunan kasar daga cikin jerin bayan ta hau mulki.
Wannan sabuwar sanarwar ta zo ne bayan watanni da dama na matsin lamba daga wasu ’yan majalisar dokoki na Amurka da suka nemi shugaban kasa da sakataren harkokin waje, Marco Rubio, su maido da Najeriya cikin jerin.
Me ake nufi idan kasa ta shiga CPC?
Kasar da aka sanya cikin jerin CPC ita ce wadda ke nuna tsananin wariya ko cin zarafi bisa dalilin addini, ko kuma wadda ke da tsarin da ke nuna rashin mutunta ’yancin yin addini.
Wannan matsayin ana bada shi ne ta hannun ministan harkokin wajen Amurka, da izinin shugaban kasa, bisa tsarin dokar Amurka ta International Religious Freedom Act (IRFA) ta shekara ta 1998.
Dokar ta IRFA ta bayyana munanan take hakkin addini kamar haka:
- Azabtarwa ko hukunci mai raɗaɗi da wulakanci
- Tsare mutum na dogon lokaci ba tare da tuhuma ba
- Haddasa bacewar mutane ta hanyar daukewa ko dogon tsarewa don batar da su
- Kowane irin keta hakkin rayuwa, ’yanci, ko tsaron mutum
Shin sauran kasashe na amfani da CPC?
Sanya kasashe cikin jerin masu hana 'yancin addini, tsari ne kawai na musamman wanda kasar Amurka ta bullo da shi.
Babu wata kasa ko kungiya ta duniya da ke amfani da irin wannan sunan da tsarin hukuncinsa.
Menene tasirin wannan matsayin?
Lokacin da Amurka ta saka wata kasa cikin jerin CPC, ana sanar da majalisar dokoki don ɗaukar matakan siyasa masu ƙarfi.
Yawancin wadannan matakan ba na tattalin arziki ba ne, don matsa lamba har sai an dakatar da cin zarafin addini.
Idan matakan farko sun gaza, sai a ɗauki matakan tattalin arziki.
Waɗannan matakan na iya haɗawa da:
- Gwamnatin Amurka ta yi tir da kasar a bainar jama’a
- Dakatar da bada tallafi
- Rage taimako kan tsaro
- Hana lamunin kuɗi daga kungiyoyin kasa da kasa
- Dakatar da lasisin fitar da kaya

Kara karanta wannan
Hana shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad ya yi martani mai zafi kan sanatan Amurka

Source: Twitter
Takunkumi kan Najeriya saboda CPC a 2020
Duk da cewa Amurka ta saka Najeriya cikin jerin CPC a 2 ga Disamba, 2020, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ba ta sanya takunkumi ba.
Ta bayyana cewa cewa hakan yana cikin muhimmiyar manufar kare muradun kasar Amurka.
A lokacin da hakan ta faru, Marigayi Muhammadu Buhari ne shugaban Najeriya, kuma ba a dade bayan hakan ba Joe Biden ya doke Trump a zaben Amurka.
Waɗanne ƙasashe ne aka sanya su CPC a baya?
A cikin jerin kasashen da aka ƙara a shekarar 2023, sun haɗa da:
- Burma (Myanmar)
- China
- Cuba
- Eritrea
- Iran
- Korea ta Arewa
- Nicaragua
- Pakistan
- Russia
- Saudi Arabia
- Tajikistan da
- Turkmenistan.
Trump ya yi barazana ga Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar daukar kwakkwaran mataki kan Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
Shugaba Trump ya yi barazanar kawo farmakin sojoji tare da dakatar da tallafin kasashen waje, idan har ba a daina kashe Kiristoci a Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne duk da cewa gwamnatin tarayya ta fito ta musanta cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

