'Yan NNPP Sun Bar Kwankwasiyya, Mutum 1000 Sun Koma APC a Kano

'Yan NNPP Sun Bar Kwankwasiyya, Mutum 1000 Sun Koma APC a Kano

  • Wasu yan jam’iyyar NNPP sama da 1,000 sun sauya sheƙa daga jam'iyya mai mulki a Kano saboda wasu dalilai guda uku
  • Wadanda suka saura shekan sun yaba da ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ke bazawaa Najeriya da jihar Kano
  • Sun kuma sanar da cewa daga yanzu sun karbi shahadar APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Akalla yan jam’iyyar NNPP tafiyar Kwankwasiyya ne suka sauya sheƙa daga jam’iyyarsu zuwa APC a jihar Kano.

Taron sauya sheƙar ya gudana a dakin taro na Fine Time da ke cikin birnin Kano, inda suka bayyana cewa sun yanke wannan shawara na ficewa daga NNPP saboda dalilai.

Kara karanta wannan

ADC ta samu karuwa a Kano, tsohon dan majalisa ya fice daga APC zuwa jam'iyyar

Barau ya karbi 'yan NNPP a Kano
Barau Jibrin tare da wasu 'yan Kwankwasiyya da suka sauya sheka Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa sun ce dalilan sun hada da nasarorin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin wajen ciyar da kasa gaba.

Barau ya karbi 'yan Kwankwasiyya a Kano

Daily Post ta wallafa cewa mai ba wa mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin labarai, Ismail Mudashir, ne ya tabbatar da sauya shekar a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Ta cikin sanarwar, Ismail ya ce masu sauya sheƙa sun bayyana cewa sun yanke shawarar rungumar APC ganin yadda jam'iyyar ke kara samun karɓuwa sosai.

'Yan kwankwasiyya 1000 sun koma APC
Hotn Sanata Barau I Jibrin a karbar 'yan Kwankwasiyya Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Shugaban tawagar da suka sauya sheƙar, Aminu Minjibir, ya bayyana cewa sun yi aiki tukuru wajen ganin nasarar tafiyar Kwankwasiyya.

Ya koka da cewa amma daga baya suka fahimci cewa NNPP ba ta iya gudanar da wani taro a babban birnin tarayya, inda daruruwan mambobin jam’iyyar NNPP, masu alaka da tsarin “Kwankwasiyya”,a cika alƙawuranta ga al’ummar Kano ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karbi 'yan majalisa 3 da wasu manyan jiga jigai da suka koma APC a Kaduna

Barau ya yabi sababbin 'yan APC

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin, wanda ya karɓe su, ya bayyana matakin da suka ɗauka a matsayin mai matuƙar kyau da dacewa, yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta fara yin rauni a siyasar jihar Kano.

A kalamansa:

“Ku yi imani da cewa kun yanke shawarar da ta dace. APC ita ce jam’iyya mafi girma a Afrika, wacce ke ɗaukar nauyin cigaban dan Adam da ci gaban ƙasa baki ɗaya."

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakai masu kyau wajen inganta rayuwar ‘yan ƙasa, musamman a bangaren ilimi, lafiya da bunƙasar tattalin arziki.

Aminu Minjibir da sauran wadanda suka koma APC sun sha alwashin yin aiki tuƙuru don ƙarfafa APC a Kano da tabbatar da nasarar ta a zabukan gaba.

'Yan kwankwasiyya sun rabu da Kwankwaso

A wani labarin, mun wallafa cewa an gudanar da wani taro a babban birnin tarayya, inda daruruwan mambobin jam’iyyar NNPP dake a kan tafarkin Kwankwasiyya suka koma APC.

Kara karanta wannan

Sanatan Kaduna, Barista Katung ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Sun bayyana cewa ficewar ta biyo bayan tattaunawa da shugabanninsu, inda suka nuna gamsuwa da yadda APC ke kokarin kare muradun jama’a da aiwatar da ayyukan more rayuwa.

Taron ya samu jagorancin Sanata Barau Jibrin, inda ya jaddada cewa APC za ta ci gaba da hada kai da al’umma, tare da tabbatar da cewa ba za a bari jama’a su ji kunya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng