Zargin Kashe Kiristoci: Zakzaky Ya Yi wa Trump Martani kan Kawo Hari Najeriya

Zargin Kashe Kiristoci: Zakzaky Ya Yi wa Trump Martani kan Kawo Hari Najeriya

  • Kungiyar IMN ta 'yan Shia'a ta ce zargin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan kisan Kiristoci karya ne
  • IMN ta ce matsalolin da suka addabi Najeriya sun ta’allaka ne da siyasa da cin hanci da rashawa, ba addini ba
  • Kungiyar ta gargadi ’yan Najeriya da su guji kururuwar kasashen Yamma da ke neman raba Musulmi da Kiristoci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kungiyar IMN karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ta karyata ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, cewa ana kisan kiyashi ga Kiristocin Najeriya.

A wata sanarwa da jami'in kungiyar, Abdullahi Danladi ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana zargin a matsayin karya, mai tayar da hankali, kuma hadari ga zaman lafiya.

Ibrahim Zakzaky
Shugaban kungiyar IMN, Ibrahim Zakzaky. Hoto: Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Source: Facebook

The Cable ta rahoto ya ce kungiyar ta dade tana fafutukar tabbatar da adalci, zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar kasar ba tare da la’akari da addini, kabila ko siyasa ba.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Matsalar Najeriya ba ta addini ba ce' — IMN

A sanarwar, Abdullahi Danladi ya bayyana cewa matsalolin Najeriya ba na addini ba ne, illa na siyasa da sauransu.

Kungiyar IMN ta ce cin hanci, son kai, da zaluncin shugabanni ne tushen rashin tsaro, ba batun addini ba.

Ya nakalto kalaman Zakzaky yana cewa:

“Talakan Kirista da talakan Musulmi ba su gaba. Abin da ke cutar da su shi ne tsarin zalunci da ya addabi kowa.”

Martanin Zakzaky ga Donald Trump

Kungiyar ta soki kalaman Trump da ke cewa “Musulmai masu tsattsauran ra’ayi” na kashe Kiristoci, tana mai bayyana hakan a matsayin dabarar kasashen Yamma don haifar da rikici a Najeriya.

Danladi ya ce irin wadannan labaran karya suna amfani ne wajen ingiza son kai da kuma ba da hujjar tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin wasu kasashe.

Ya kara da cewa Musulmai da Kiristoci duka sun fuskanci hare-hare daga ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da ‘yan bindiga — abin da ke nuna matsalar ba ta addini ba ce.

Kara karanta wannan

Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

'Kasashen Yamma na rashin adalci,' IMN

IMN ta zargi wasu shugabannin kasashen Yamma da nuna rashin gaskiya, tana cewa su ne suka tallafa wa rikice-rikicen da suka addabi kasashen Musulmai a baya kafin fara magana kan Najeriya.

Ya ce irin wannan lamari na iya haddasa gaba tsakanin addinai a Najeriya, inda ya jaddada cewa IMN tana ci gaba da karfafa tattaunawa da hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Ibrahim Zakzaky ya nemi a hada kai

Danladi ya ce Zakzaky ya bukaci ’yan Najeriya da su ki amincewa da labaran rarrabuwar kawuna daga waje, su mayar da hankali wajen yaki da cin hanci da rashin gaskiya.

Daily Post ta wallafa cewa kungiyar IMN ta kuma tabbatar da jajircewarta wajen ganin an samu zaman lafiya, adalci, da hadin kai a Najeriya.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|Donald J Trump
Source: Twitter

Ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani yunkuri na kasashen waje da ke neman haddasa gaba a tsakanin al’ummar Najeriya.

Amurka za ta sakawa gwamnoni takunkumi

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka ya taso Najeriya, zai gabatar da kudirin hana shari'ar musulunci da batanci

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka za ta yi bincike kan zargin tauye 'yancin addini a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan zargin kisan Kiristoci da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi a makon da ya wuce.

Hasashe ya nuna cewa gwamonin jihohi, sarakuna da alkalai za su iya fuskantar takunkumi daga kasar Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng