Shari'a: Gwamnoni, Sarakuna da Wadanda Amurka za Ta iya Sakawa Takunkumi

Shari'a: Gwamnoni, Sarakuna da Wadanda Amurka za Ta iya Sakawa Takunkumi

  • Majalisar dokokin Amurka na duba kudirin da zai sanya takunkumi kan wasu gwamnoni, alkalan kotuna da sarakunan Najeriya
  • Kudirin na zargin jami’an Najeriya da laifin goyon bayan “cin zarafin addini” da kuma aiwatar da dokar Shari’a a wasu jihohi
  • Gwamnatin Najeriya ta maida martani, tana kare tsarin mulki da dokokinta na ’yancin addini ba tare da tsangoma ga kowa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar dokokin Amurka na duba yiwuwar sanya takunkumi kan gwamnoni da wasu manyan jami’an gwamnati bisa zargin cin zarafin ’yancin addini a Najeriya.

Wannan batu na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana damuwa game da zargin kisan Kiristoci a kasar.

Shugaba Bola Tinubu, Donald Trump
Shugaban Najeriya da na Amurka, Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga|Donald Trump
Source: Twitter

Kudirin, wanda Sanata Ted Cruz ya dauki nauyi kuma ya wallafa a X, na neman hukunta duk wanda ya goyi bayan dokar ya a tunaninsa tana tauye ’yancin addini a kasar.

Kara karanta wannan

Jihohin da za su jikkata idan Amurka ta farmaki Najeriya da sunan yaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda Amurka za ta bincika a Najeriya

Kudirin da aka gabatar a ranar 9, Oktoba, 2025, na kira da a sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke fuskantar takunkumin Amurka saboda take ’yancin addini.

A kudirin, ministan harkokin wajen Amurka zai gabatar da rahoto cikin kwana 90 da zai fadi dukkan jami’an Najeriya da ake zargin da hannu wajen aiwatar da dokokin batanci ko tauye ’yancin addini.

Takunkumin zai kasance bisa dokar Executive Order 13818, wanda ke iya haifar da haramcin tafiya zuwa Amurka, rike kadarori da takaita hulɗar kudi.

Rahoto ya ce binciken zai bi ta kan gwamnoni, sarakuna, alkalai da masu ruwa da tsaki a garuruwan da aka kafa Shari'a.

Tarihin dokar Shari’a a Najeriya

Kudirin ya mayar da hankali kan aiwatar da dokar Shari’a a wasu jihohin Arewa, yana kiran hakan “dokar batanci” da ke cutar da Kiristoci.

Sai dai Shari’a ta kasance tsarin dokar Musulunci tun kafin mulkin farar hula a 1999, lokacin da Zamfara karkashin Ahmad Sani Yerima ta fara fadada aikinta.

Kara karanta wannan

Hana shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad ya yi martani mai zafi kan sanatan Amurka

Bayan shekaru biyu, jihohi kamar Kano, Katsina, Sokoto, Bauchi, sun bi sahu, yayin da wasu kamar Kwara, Kogi, da Benue suka ci gaba da amfani da tsarin dokar gargajiya.

Martanin gwamnatin tarayya kan sharia'a

Punch ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zargin, tana mai cewa tsarin mulkin kasar bai tilasta bin wata doka ta addini ba.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje ta fitar, gwamnati ta ce duk dokokin jihohi, ciki har da na Shari’a, suna karkashin tanadin kundin tsarin mulki.

Ministan harkokin wajen Najeriya
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. Federal Ministry of Foreign Affairs
Source: Twitter

Zancen ganawar Tinubu da Trump

A wani rahoton, kun ji cewa Daniel Bwala ya bayyana cewa Bola Tinubu zai gana da Donald Trump domin tattauna zargin kisan Kiristoci da kuma hadin kai kan yaki da ta’addanci.

Bwala ya ce shugaban kasa Tinubu da Trump suna da manufa daya a yaki da ta’addanci da duk wani abu da ke barazana ga bil’adama.

Ya kara da cewa Trump ya taimaka wa Najeriya wajen samun makamai, kuma gwamnatin Tinubu na amfani da damar don tabbatar da tsaro a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng