Tsohon Minista Ya Kausasa Harshe, Ya Zargi Trump da Kokarin Raba Najeriya
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi Allah-wadai da barazanar da Donald Trump ya yi na kawo wa Najerita hari
- Ya zargi shugaban Amurka da ƙoƙarin haifar da rikicin addini a Najeriya, wanda hakan zai rikirkita kasar domin neman samun albarkatun ƙasa
- Fani-Kayode ya kira ‘yan Najeriya su haɗa kai, su kare ƙasarsu daga azzaluman dake shirin kawo hatsaniyar da sai kowa ya ji a jikinsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya mayar da martani mai zafi kan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump.
Kakkausan martaninsa ya zo ne bayan da Trump ya yi barazanar cewa Amurka na iya ɗaukar matakin soja kan Najeriya kan zargin kisan Kiristoci a ƙasar.

Kara karanta wannan
Yadda ta kaya tsakanin Buhari da Trump a fadar White House kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Source: Facebook
A wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Fani-Kayode ya bayyana kalaman Trump da cewa abin kunya kuma ƙoƙarin haifar da rikicin addini a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Fani Kayode ya caccaki Donald Trump
Tsohon Ministan ya dauki zafi sosai, inda ya bayyana Trump a matsayin azzalumi, wanda ke yi wa Najeriya barazana da sunan kawo dauki ga kirisoci.
Ya bayyana cewa:
“Mahaukaci, azzalumi dake jiji da kai kamar Shugaba Donald Trump yana barazana ga ƙasarmu da tashin hankali da mamaya. Wannan rashin kunya ne.”
Fani Kayode ya kara da cewa babu gudu, babu ja da baya matukar Trump ya tabbatar da yunkurinsa a kan Najeriya, za su yi tsayin daka wajen tsayawa da kasarsu.
Ya ce:
“Idan ya aiwatar da wannan barazana, za a yi yaƙi. Ba za mu gudu ba, za mu tsaya mu kare ƙasarmu.”
FFK: Donald Trump dan son zuciya ne
Tsohon Ministan ya kuma zargi Trump da rashin gaskiya da son zuciya, inda ya ce Shugaban Amurka bai iya magana a kan shugabannin da ke haddasa kashe-kashe a Sudan da Gaza ba.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya

Source: Twitter
Fani-Kayode ya yi gargadi cewa duk wani hari daga ƙasashen waje ba zai raba tsakanin Musulmi da Kirista ba, yana mai cewa:
“Bam da makaman yaƙi ba sa bambanci tsakanin addinai ko kabilu. Idan aka fara harbi, kowa zai mutu ko ya gudu.”
Ya kuma zargi Amurka da ƙoƙarin sake mulkar mallaka ta hanyar neman albarkatun ƙasa da ma’adinai a kasar nan.
A kalamansa:
“Wannan duk ba don addini ba ne, sai don samun albarkatun ƙasarmu."
Femi Fani Kayode ya kara da kira ga 'yan Najeriya da su hada kai, su zama tsintsiya madaurinki daya yayin da ake yiwa kasarsu barazana daga waje.
Trump ya aiko da sako ga Tinubu
A baya, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake aiko da gargadi ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a kan zargin cewa ana yiwa kiristoci kisan gilla.
'Dan majalisar kasar, Riley M. Moore, ya bayyana cewa Amurka ba za ta yi shiru a kan kisan da ta hakikance ana yi ba, duk da cewa kasar da masu ruwa da tsaki sun karyata haka.

Kara karanta wannan
Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci
Moore, ya shaida cewa Trump ya umarce shi da ya sanar da gwamnatin Najeriya cewa dole ne ta hada kai da Amurka a kan batun ko a dauki matakin da ya dace a kan kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng