Taraba: Gwamna Ya ba da Umarni kan Rigimar Masallacin Juma’a da Aka Rasa Rai
- Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya rufe masallacin Juma'a a Donga bayan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu
- Kefas ya ce gwamnati za ta gina sababbin masallatai uku domin kungiyoyin Izalah da kuma Darika, don tabbatar da adalci da zaman lafiya.
- Shugabannin addini da al’umma sun yaba wa matakin gwamnan, tare da yin addu'a domin dorewar zaman lafiya a Taraba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya shiga lamarin rigimar da ta afku game da masallacin Juma'a a jihar.
Gwamnan ya rufe wani masallacin Juma’a da ake ta ce-ce-ku-ce a kai a Donga bayan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu da jikkata wasu da dama a yankin.

Source: Twitter
Gwamna Kefas ya kawo karshen rigima kan masallaci

Kara karanta wannan
Kwamandojin 'yan bindiga sun kaure da fada, shedanin dan ta'adda ya sheka barzahu
Wannan umarni ya zo ne yayin babban taron zaman lafiya da ya jagoranta tare da shugabannin gargajiya, malamai, shugabannin al’umma, matasa da wakilan mazhabobin musulunci, cewar Ledership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya gudana ne a fadar mai martaba Sarkin Gara Donga, inda gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, daidaito da zaman lafiya tsakanin addinai a jihar.
Ya ce taron na da muhimmanci domin magance sabanin da aka dade ana samu tsakanin mabiya dariku daban-daban na musulunci a yankin.
Gwamna Kefas ya bayyana cewa za a rufe masallacin Juma'an na dan lokaci har sai gwamnati ta gina sababbin masallatai uku, ga Izalar Jos, Izalar Kaduna da Darika.
Ya ce hakan zai tabbatar da adalci, zaman lafiya da ‘yancin kowa na ibada, ya kuma kara da cewa Kiristoci ma karkashin CAN ba za a manta da su ba a kokarin tabbatar da daidaito.

Source: Original
Gargadin da Gwamna Kefas ya yi a Taraba
Gwamnan ya yi gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da duk wani abu da zai lalata zaman lafiya ba.
Ya ce addini bai koyar da kiyayya ba, sannan adalci shi ne ginshikin zaman lafiya, ya yi kira da a tuba daga rarrabuwar kawuna, a rungumi juna da hakuri domin ci gaban Donga da Taraba baki daya.
A jawabansu, shugabannin musulunci, Malam Musa, Malam Rabiu na Darika, Malam Sabo na Izala-Jos da Malam Ma’awiyya na Izalar Kaduna, sun yaba wa gwamnan bisa hikima da adalci, tare da alkawarin hada kai domin zaman lafiya.
Sarkin Donga shi ma ya gode wa gwamnan bisa fifita tattaunawa maimakon rarrabewa.
An kammala taron da addu’o’i na hadin gwiwa tsakanin Musulmi da Kirista domin neman jagoranci daga Allah da zaman lafiya mai dorewa a Taraba.
Gwamna ya yi huduba a masallacin Juma'a
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a a karamar hukumar Kokona.
Rahoto ya nuna cewa an gina masallacin ne karkashin kulawar kwamishinan ilimi na jihar, Dr. John D.W. Mamman.
'Yan siyasa, sarakunan gargajiya da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu sun halarci bude masallacin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
