Kisan Kiristoci: Sanata Ndume Ya Dora Laifi kan Gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa

Kisan Kiristoci: Sanata Ndume Ya Dora Laifi kan Gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa

  • Sanata Ali Ndume ya ce sakacin Gwamnati da Majalisa ne suka jawo saka Najeriya a jerin kasahen da ke ba matsalr 'yancin addini
  • A jiya Juma'a, Shugaba Donald Trump na Amurka ya maida sunan Najeriya cikin jerin wadannan kasashe saboda zargin kisan kiristoci
  • Ali Ndume ya ce tun farko ya hango wannan matsalar kuma ya ankarar da gwamnatin Bola Tinubu da Majalisa amma suka yi biris

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya tsoma baki kan matakin Amurka na sanya Najeriya cikin kasashen da ke da matsala kan yancin addini.

Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya dora laifin sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke da “babban matsala kan ’yancin addini” kan gwamnatin Shugaba Bola da Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Sanata Ali Ndume.
Hoton Sanata Ali Ndume a Majalisar Dattawa Hoto: Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ndume ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya zargi gwamnati da Majalisa

Sanatan ya zargi bangaren zartarwa da na majalisa da sakaci, inda ya ce gazawarsu wajen tuntubar gwamnatin Amurka kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya ne ya janyo hakan.

Ndume ya ce tun farko ya gabatar da kudiri a majalisa kan zargin “kisan gillar Kiristoci," wanda ya sa aka yanke shawarar cewa gwamnatin Najeriya ta tuntubi Amurka ta gabatar mata da hujjoji da sahihan alkaluma.

A ranar Juma’a ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa Najeriya ta koma cikin jerin “Kasashen da ke da Babban Matsala Kan ’Yancin Addini” saboda zargin wariyar addini da kisan Kiristoci.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata wannan batu nan take, tana mai cewa kalaman Trump ba su nuna hakikanin halin da kasar ke ciki ba, in ji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka ya taso Najeriya, zai gabatar da kudirin hana shari'ar musulunci da batanci

Dalilan Ndume na dora laifi kan Majalisa

Amma Sanata Ndume ya ce gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa sun yi sakaci tun bayan da dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya fara magana kan batun, kafin Trump ya fitar da sanarwa.

Ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta tuntubar gwamnatin Amurka da cikakkun bayanai kan ayyukan ’yan ta’adda da ba su la’akari da addini wajen kai hare-hare.

“Na gargadi gwamnati tun farko, na gabatar da kudiri a majalisa. Najeriya kasa ce mai cikakken ’yancin kanta. Ba wai abin da Amurka za ta yi mana ba ne, amma yadda wannan kuskuren fahimta zai iya yin illa ga kasar.
"Ya kamata mu tunkari gwamnatin Amurka ta hanyar gabatar da sahihan bayanai da alkaluma, mu nemi su saurari bangaren gwamnati da na al’ummar Musulmai. Musulmai ma ana kashe su.
Wannan kisan gillar ba ga Kiristoci ba ne kawai, ’yan Najeriya gaba ɗaya ne lamarin ya shafa."

- Sanata Ali Ndume.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya dora alhakin kisan Kiristoci a Najeriya kan Jonathan a 2014

Shugaba Tinubu da Ndume.
Hoton Shugaba Bola Tinubu a Aso Rock da na Sanata Ali Ndume a zauren Majalisar Dattawa Hoto: @OfficialABAT, Ali Ndume
Source: Facebook

Tinubu ya maida martani ga Trump

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce Najeriya tana mutunta kowane addini kuma ba ya yarda da cin zarafi ba.

Bola Tinubu ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da kansa a matsayin martani ga shugaban Amurka, Donald Trump.

Shugaban ya ce Najeriya kasa ce da ke bin tsarin dimokuradiyya wanda ya bai wa kowane dan kasa dama da yancin addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262