Tinubu Ya Maida Martani ga Shugaban Amurka, Trump kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

Tinubu Ya Maida Martani ga Shugaban Amurka, Trump kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya musanta ikirarin takwaransa na Amurka, Donald Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
  • Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce da ke mutunta kowane addini kuma tana kokarin inganta zumunci tsakanin al'ummarta
  • Ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da Amurka da sauran kasashen duniya wajen kare yancin addini ga kowane dan kasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani kai tsaye ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Sanata Ndume ya dora laifi kan gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa

Bola Tinubu ya fito karara ya fada wa Shugaba Trump cewa Najeriya ba ta lamuntar wariya ko cin zarafin kowane addini a kasar.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, a matsayin martani ga takwaransa na Amurka, Donald Trump.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da shugaban Amurka ya yi

A jiya Juma'a ne Shugaba Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin “Kasashen da ke da Babban Matsala kan ’Yancin Addini.”

Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana ta rayuwa, inda ya ce Amurka za ta dauki mataki don kare su.

“Kiristanci na fuskantar barazanar bacewa a Najeriya, ana musu kisan kare dangi," in ji Trump.

Tinubu ya maida martani ga Trump

A martaninsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mulkin dimokuradiyya wacce take bin kundin tsarin mulki da ke tabbatar da ’yancin addini ga kowa.

A ruwayar Daily Trust, Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Kisan Kiristoci: 'Rayukan Musulmi ma suna da daraja': Hadimin Tinubu ga Amurka

“Najeriya na nan a matsayin kasa mai bin tsarin dimokuradiyya, wacce kundin tsarin mulkinta ke bayar da cikakken ’yancin addini.
"Tun 2023, gwamnati ke gudanar da tattaunawa da hadin kai tsakanin shugabannin Kiristoci da Musulmai, tana kuma ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ’yan kasa ba tare da la’akari da addininsu ko yankin da suka fito ba."

Da gaske ana kashe kiristoci a Najeriya?

Tinubu ya ce zargin da ake na yi wa kiristoci kisan kiyashi ba gaskiya ba ne, domin bai nuna hakikanin yanayin kasar ba, kuma bai la’akari da kokarin gwamnati na tabbatar da ’yancin yin addini ga kowa da kowa ba.

“’Yancin addini da ra’ayoyi daban-daban wani ginshiki ne na hadin kanmu a matsayin kasa, kuma hakan zai ci gaba da kasancewa.
"Najeriya ba ta goyon bayan zaluntar wani addini, balle kuma ta karfafa irin hakan. Najeriya kasa ce da kundin tsarin mulkinta ke kare ’yancin kowane dan kasa.
"Gwamnatina za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin Amurka da sauran kasashen duniya wajen zurfafa fahimtar juna da hadin gwiwa domin kare masu bin addinai daban-daban.”

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka ya taso Najeriya, zai gabatar da kudirin hana shari'ar musulunci da batanci

- Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu da Donald Trump.
Hoton Shugaba Bola Ahmed da na takwaransa na kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Sanatan Cruz na son han shari'ar musulunci

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ted Cruz na kasar Amurka ya sha alwashin gabatar da kudiri domin haka aiwatar da dokokin shari'ar Musulunci da batanci a Najeriya.

Ya ce wannan mataki ya yi daidai da kokarinsa na kare yancin Kiristocin da ake zargin ana zalunta ta hanyar yi masu kisan kare dangi a Najeriya.

Ya kara da cewa kudirin da zai gabatar zai tanadi takunkumi da matakan ladabtarwa ga jami’an Najeriya da ke aiwatar da ko goyon bayan dokokin batanci da shari’ar musulunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262