Kisan Kiristoci: 'Rayukan Musulmi ma Suna da Daraja': Hadimin Tinubu ga Amurka

Kisan Kiristoci: 'Rayukan Musulmi ma Suna da Daraja': Hadimin Tinubu ga Amurka

  • Zargin Kisan kiyashin da aka ce ana yi wa Kiristoci na ci gaba da jawo muhawara a Najeriya a yan kwanakin nan
  • Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yi martani ga gwamnatin kasar Amurka kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
  • Ya ce Amurka ta yi kuskure a zargin kisan Kiristoci a Najeriya inda ya ce hare-haren ta’addanci ne da suka shafi kowa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga, ya nuna damuwa kan yada zargin kisan kiristoci a Najeriya.

Onanuga ya bayyana an kai hare-haren ne ba tare da duba bangaranci ba inda ya shafi dukkan addinai da ake da su a Najeriya.

Hadimin Tinubu ya soki Amurka kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu. Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Rahoton Tribune ya ce Onanuga ya bayyana cewa rayukan Musulmai ma suna da muhimmanci inda ya kalubalanci zarge-zargen da ake yi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da ake yi na kisan Kiristocin Najeriya

Sanata Marco Rubio ya yi ikirarin cewa ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya wanda ya ce ana kokarin karar da su ne a kasar.

Ya ce wannan abu ne mai tayar da hankali kuma Amurka za ta dauki mataki domin tabbatar da kare Kiristoci da addinsu.

Rubio ya wallafa cewa Fulani da kungiyoyin Musulmai masu tsattsauran ra’ayi na kashe Kiristoci, ya bayyana cewa Amurka na shirye ta dauki matakin kariya.

Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Amurka kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya karyata zargin kisan Kiristoci

Bayo Onanuga ya karyata wannan batu inda ya ce babu wani kisan kiyashi na Kiristoci, kuma bayanin da ake yadawa almara ce ta siyasa.

Ya ce ayyukan ta’addanci suna faruwa ne a wasu yankuna, inda ‘yan ta’adda da barayi ke kai hare-hare ba tare da bambanci ba kan Musulmi da Kirista.

Onanuga ya jaddada cewa ana kai hare-hare kan majami’u da masallatai, ya ce ba addini suke bi ba, domin suna kai farmaki ba tare da bambanci ba.

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka ya taso Najeriya, zai gabatar da kudirin hana shari'ar musulunci da batanci

Abin da Najeriya ke bukata daga Amurka

Onanuga ya kara da cewa abin da Najeriya ke bukata daga Amurka shi ne taimakon sojoji domin yakar ‘yan ta’adda, ba rarraba kawuna ba ko daukar mataki a kasar ba.

A wani sako, ya sake tabbatar da cewa babu kisan gilla kan Kiristoci, ya roki Amurka ta fahimci gaskiya da taimakawa wajen tsaro, cewar Daily Post.

Ya ce Najeriya ta fi bukatar tallafin sojoji, kayan tsaro da hadin kai, domin kare al’umma a jihohin Arewa da sauran yankuna masu fama da barazana.

Kisan Kiristoci: Yadda Tinubu ya zargi Jonathan

Kun ji cewa zargin yi wa al'ummar Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce da muhawara mai zafi a sassa daban-daban na duniya.

Wannan ya kara kamari ne bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya cikin kasashe masu matsala ta musamman kan batun cin zarafin Kiristoci.

A shekarar 2014, Shugaba Bola Tinubu ya taba sukar Goodluck Jonathan lokacin yana shugabancin Najeriya bayan an farmaki wasu al'ummomin Kiristoci a Arewacin kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.