Zargin Kifar da Tinubu: 'Dan Majalisa Ya Shiga Kotu da Rundunar Sojoji
- 'Dan majalisa dag Osun ya gurfanar da rundunar sojojin Najeriya a kotu bisa zargin yunkurin juyin mulki da kifar da gwamnati
- 'Dan siyasar wanda kuma lauya ne ya ce babu kundin kasa ko dokar sojoji da ta ba rundunar ikon kwace mulki daga gwamnatin farar hula
- Ya bukaci kotu ta hana rundunar sojoji duk wani yunkuri na karbar mulki da karfin tuwo a nan gaba saboda kare dimukradiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a Najeriya na ci gaba da jawo maganganu da mabambantan ra'ayoyi.
Wani dan majalisar dokoki na jihar Osun, Kanmi Ajibola, ya shigar da rundunar sojojin Najeriya kara a kotu bisa zargin yunkurin juyin mulki domin kifar da gwamnati.

Source: Getty Images
Juyin mulki: 'Dan majalisa zai shiga kotu
Rahoton The Guardian ya ce an yi ta yada cewa an yi yunkurin kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki da karfi a watan Oktobar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajibola, wanda lauya ne kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi reshen Ilesa, ya kalubalanci rundunonin tsaro kan zargin da ake yi.
Daga cikin wadanda ya maka a kotu akwai rundunar sojojin kasa, rundunar sojojin saman, rundunar sojojin ruwa da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
Yaushe aka maka rundunar sojoji a kotu?
'Dan majalisar ya shigar da korafin ne a ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, a kotun tarayya da ke birnin Osogbo a jihar Osun.
A cikin korafin da ya shigar, ya bayyana cewa babu wani sashe a kundin tsarin mulki ko dokar sojoji da ya ba kowane sashe na rundunar ikon kwace gwamnatin farar hula.
Ya ce sashen 217 (2) na kundin tsarin mulki ya bayyana aikin rundunar, kuma babu inda aka ba su damar aikata wani aiki da ya sabawa dokokin mulkin dimokuraɗiyya.

Source: Facebook
Abin da doka ta ce kan juyin mulki
Ajibola ya kuma jaddada cewa doka ta wajabta ga sojoji bin sashen 1 (2), 150 da 217 na Kundin 1999 da kuma sashen 1 (3-5) na dokar sojoji, don haka ya roki kotu ta hana su daukar mulki ko yin juyin mulki ta kowace hanya da kundin bai amince da ita ba.
Ya ce wannan zargin juyin mulki da aka ruwaito kwanan nan abin takaici ne kuma kalubale ga mahalarta gwagwarmayar farfado da dimokuraɗiyya a Najeriya.
Dan majalisar ya ce har yanzu yana da imani cewa wadannan jami’an da ake zargi da yunkurin juyin mulkin “suna cikin kuskuren tunanin cewa su na da ikon kwace mulki daga hannun gwamnati.”
Ya kara da cewa kasancewarsa lauya kuma dan kasa, doka ta bashi damar gabatar da kara domin kare tsarin mulkin dimokuraɗiyya a kasar, cewar Daily Post.
Sojoji 2 sun tsere saboda argin juyin mulki
An ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami’ai biyu sun tsere bayan sun shiga cikin jerin wadanda ake zargi da shirin juyin mulki.
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an da suka tsere sun hada da wani Manjo daga jihar Taraba da kuma daya daga birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa sama da jami’an sojoji 30 yanzu suna tsare da ake bincike kan zargin juyin mulki wanda ya ta da hankula a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

