Yadda aka Sace Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi bayan Fita daga Sallah a Masallaci
- Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta tabbatar da sace mataimakin shugaban majalisar jihar, Alhaji Muhammad Sama’ila Bagudu
- Rahoton 'yan sanda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da daddare, bayan sallar Isha’i, a karamar hukumar Bagudu
- Biyo bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda tare da sojoji da jami’an sa-kai sun fara aikin ceto domin kubutar da dan majalisar jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mataimakin shugaban majalisar jihar.
An sace Alhaji Muhammad Sama’ila a Bagudu, hedikwatar karamar hukumar Bagudu, da misalin karfe 8:20 na dare a ranar Juma’a, 24, Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Tashar NTA ta wallafa a X cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Birnin Kebbi.
Ya ce, an kai harin ne bayan Hon. Bagudu ya idar da sallar Isha’i kuma yana kan hanyarsa ta dawowa gida.
Rahotanni sun nuna cewa mai magana da yawun gwamnan jihar, Ahmed Idris, ya tabbatar da samun labarin sace dan majalisar, yana mai cewa gwamnati ta dauki mataki.
Rundunar ‘yan sanda ta dauki mataki
CSP Abubakar ya bayyana cewa rundunar ta dauki matakin gaggawa ta hanyar tura tawagar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda, sojoji, da masu sa-kai domin bin sawun ‘yan bindigar.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Tawagar hadin gwiwar na ci gaba da sintiri da bincike a cikin dazuka da hanyoyin da ake zargin ‘yan bindigar suka bi domin ceto dan majalisar ba tare da wani lahani ba, tare da cafke wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.”
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello Sani, ya tabbatar da kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kiran 'yan sanda ga jama'ar Kebbi
Abubakar ya bukaci al’umma su kasance masu sa ido da bayar da rahotanni kan duk wani motsi da suka ga yana da hadari.

Source: Facebook
Ya ce:
“Kwamishina ya roki jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar,”
Har zuwa yanzu ba a ji daga bakin ‘yan bindigar ba game da bukatunsu a kan kudin fansa ko yadda za su saki mataimakin shugaban majalisar ba.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da amfani da dukkan dabaru da kayan aikin da ke hannunta har sai an ceto Hon. Sama’ila Bagudu lafiya.
Najeriya ta karyata zargin kisan kare dangi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta karyata zargin kisan kiyashi da shugaban Amurka ya ce ana yi wa Kiristoci.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa 'yan ta'adda na kashe mutane ba tare da lura da addininsu ba.

Kara karanta wannan
'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta cigaba da mu'amala da Amurka wajen yaki da rashin tsaro domin kawo zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

