Shugaba Tinubu Ya Nada Gwamnan Kwara da Wasu Gwamnoni 6 a Mukamai na Musamman

Shugaba Tinubu Ya Nada Gwamnan Kwara da Wasu Gwamnoni 6 a Mukamai na Musamman

  • Shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya samu mukami a kwamitin aiwatar da shirin RHWDP
  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Gwamna AbdulRazaq a matsayin shugaban kwamitin, ya kuma bai wa gwamnoni shida mukamai
  • Tinubu ya kirkiro shirin ne domin tabbatar da kowane dan kasa ya amfana da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq a mukami.

Shugaba Tinubu ya nada Gwamna Abdulrazaq a matsayin Shugaban Kwamitin da zai Jagoranci Aiwatar Shirin Raya Mazabu na Renewed Hope (RHWDP).

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Tinubu yana aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Dalilin Tinubu na kirkiro shirin RHWDP

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta fitar yau Juma'a, 31 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

APC ta jero sunayen gwamnan Filato da gwamnoni 3 da za su sauya sheka kafin karshen 2025

Shugaba Tinubu ya kirkiro shirin RHWDP ne domin tsara hanyoyin da za su hanzarta ayyukan ci gaba, inganta rayuwar al’umma da ƙarfafa tsarin kariyar zamantakewa a matakin ƙananan hukumomi da mazabu.

A cewar wata sanarwar, Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, shi ne zai kasance Mataimakin Shugaban Kwamitin.

Gwamnoni 6 da Tinubu ya nada a RHWDP

Mai girma shugaban kasa ya kuma naɗa wasu gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasar nan don wakiltar yankuna guda shida.

Gwamnonin da suka sami wannan mukamai sun hada da:

1. Arewa maso Gabas: Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe

2. Kudu maso Kudu: Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa

3. Kudu maso Yamma: Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.

4. Kudu maso Gabas: Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu

5. Arewa maso Yamma: Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya aika sako ga dattawan Arewa kan batun raba Najeriya

6. Arewa ta Tsakiya: Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai.

Gwamnan Kwara ya jagoranci zaman farko

A ranar Laraba da ta shige, kwamitin ya gudanar da zama na farko a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya da ke Abuja, karkashin jagorancin Gwamna AbdulRazaq.

Taron ya tattauna kan dabarun aiwatar da tsarin ci gaban gundumomi da Shugaba Tinubu ya kaddamar, wanda zai shafi gundumomi 8,809 da ke faɗin ƙasar nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna AbdulRazaq da Shugaba Tinubu.
Hoton Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq tare da Shugaba Tinubu a Aso Rock Hoto: @AARahman
Source: Twitter

Manufar shirin, kamar yadda aka bayyana, ita ce tabbatar da cewa yan Najeriya a kowane mataki sun aha romon sauyin tattalin arziki da ci gaban da gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa ta karkashin Manufar Renewed Hope Agenda.

Tinubu ya ba hafsoshin tsaro aiki

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci hafsoshin tsaro da su tashi tsaye wajen magance barazanar tsaro da ke kara tasowa a sassa daban-daban na Najeriya.

Tinubu ya ƙara da cewa ’yan Najeriya sun kosa su ga zaman lafiya da tsaro sun dawo, don haka ya bukaci hafsoshin tsaron su tashi tsaye su yaki ta'addanci.

Kara karanta wannan

ADC ta rabu gida 3 kowanne bangare ya ja daga a Adamawa

Shugaban kasar ya ce babu sauran uzuri, yanzu mutane sun zuba ido ne su ga yadda zaman lafiya da tsaron zai dawo a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262