Rahoto Ya Bankado Miliyoyin 'Yan Najeriya da Yunwa za Ta Yiwa Lahani a 2026
- Wani rahoto da Cadre Harmonisé (CH) ta fitar ya gano gagarumar barazanar rashin abinci da zai shafi jihohi akalla 27 a Najeriya
- Rahoton ya ce mutane sama da miliyan 34 za su fuskanci matsalar abinci da gina jiki mai tsanani daga Yuni zuwa Agusta 2026
- Aƙalla mutane miliyan 27.2, ciki har da 'yan gudun hijira 485,000, suna cikin mawuyacin hali tun Oktoba zuwa Disamba 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani bincike da kungiyar Cadre Harmonisé (CH) ta yi ya gano cewa mutane miliyan 34.7 a jihohi 27 da Abuja za su fuskanci matsalar abinci mai tsanani .
Rahoton da aka fitar a kan rashin abinci mai gina jiki a ranar Juma’a a Abuja ya nuna cewa lamarin zai yi kamari daga Yuni zuwa Agusta 2026.

Source: Facebook
Nigerian Tribune ta wallafa cewa Ma’aikatar noma ta Najeriya tare da goyon bayan Kungiyar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da wasu abokan aiki suka yi aiki a kan rahoton.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hango matsalar abinci a Najeriya
Business Day ta wallafa cewa Dr. Marcus Ogunbiyi, babban sakataren noma da samar da abinci ya bayyana cewa wannan sakamako na barazanar yunwa kiran gaggawa ne na a tashi tsaye.
Ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai da daukar mataki domin kare rayukan miliyoyin iyalai, musamman wadanda ke yankunan da rikice-rikice suka shafa.
A cewarsa, rahoton ya nuna cewa, duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki, matsalar abinci na ci gaba da yaduwa a kasar nan.
Rahoton ya nuna cewa sama da kashi 55 cikin 100 na gidajen da suka iya samun abinci mai inganci sun yi hakan ne ta hanyar rage cin abinci ko cin bashi.
Yankunan da za a samu matsalar abinci
Rahoton ya bayyana cewa tsadar kayayyakin abinci kamar mai, madara, nama, da kayan miya, wanda ya karu da fiye da kashi 35 cikin 100, ya yi tasiri sosai ga iyalai.

Source: Facebook
Haka kuma, rashin tsaro, tsadar kayan gona da raunin tattalin arziki a karkara suna ci gaba da tabarbarewa, wanda ke kara jefa jama'a a cikin wahala.
Manoma a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da wasu sassan Arewa ta Tsakiya sun fuskanci wahalar samun filaye sakamakon ta’addanci, garkuwa da mutane da fashi.
Yankunan Borno, Yobe, Adamawa, Katsina, da Jigawa sun kai suna daga cikin inda aka samu matsalolin isassun abinci mai gina jiki mai tsanani, yayin da wasu sansanonin 'yan gudun hijira a Binuwai.
Dr. Hussein Gadain daga FAO ya yi kira ga jihohin da ba su shiga tsarin CH ba su shiga kafin Maris 2026 domin samun cikakken rahoto.
Yaki da yunwa: An rabawa manoma injina
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya kaddamar da rabon babura guda 300 ga malaman gona domin saukaka zirga-zirga da kuma inganta noma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an raba baburan ne a matsayin rancen da ba shi da kudin ruwa, inda za a biya kudin cikin watanni 60 domin a samu damar inganta rayuwa.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa rabon baburan na cikin jimillar guda 1,700 da gwamnati ke shirin bayarwa domin tallafawa ma’aikatan gona a sassan jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


