Shafin Daukar Aikin NIS, NCDC da Hukumomi 2 Ya Fara Dawowa da Minista Ya Dauki Mataki
- Gwamnatin tarayya ta bada umarnin gyara shafin daukar aikin jami'an hukumomin shige da fice, sibil difens, ganduroba da kwana-kwana
- Hakan ya biyo bayan tsaikon da aka samu bayan hukumar CDCFIB ta fitar da sunayen wadanda suka tsallake matakin farko
- Duk wanda ya ga sunansa a cikin wannan jeri, zai zauna jarabawar tantancewa ta CBT, wanda ke cikin matakan daukar aikin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - 'Yan Najeriya da suka cike neman aikin hukumomin shige da fice, sibil difens, ganduroba da kwana-kwana sun koka kan matsalar da aka samu a shafin yanar gizo.
Sai dai Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya ba da umarnin gyara shafin cikin gaggawa domin bai wa mutane damar duba sunayensu.

Source: Facebook
Tunji-Ojo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 31 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daukar aiki: Hukumar CDCFIB ta saki sunaye
Wannan dai na zuwa ne bayan hukumar hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta saki sunayen wadanda suka tsallake matakin farko.
Hukumar CDCFIB mai alhakin daukar aikin ta fitar da sunayen wadanda ta dauka domin zana jarabawar neman daukar aiki wacce za a yi a na'ura mai kwakwalwa (CBT).
Sai dai bayan sanar da sakin sunayen, yan Najeriya sun koka kan yadda shafin ba ya tafiya idan mutum ya shigar da bayanan da aka bukata, lamarin da ya jawo hankalin ministan.
Gwamnatin Tinubu ta dauki mataki
A sanarwar da ya fitar, Olubunmi Tunji-Ojo ya umurci hukumar da ta gyara duk matsalolin fasaha da ke hana masu nema aikin damar duba sunayensu.
Ministan ya ce:
“Bayan korafe-korafen da muke samu daga masu neman aiki a hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin CDCFIB, waɗanda har yanzu ba su iya duba sunayensu ba saboda matsalolin fasaha, na ba da umarnin a gaggauta gyara lamarin."

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Yadda sojojin da aka tsare suka 'tona asirin' tsohon minista, Timipre Sylva
Tunji-Ojo ya umarci shugaban CDCFIB da ya tabbatar an kammala shigar da duk bayanan da ya kamata kuma a gyara matsalar da mutane ke fuskanta idan sun shiga shafin.
Shafin daukar aikin CDCFIB ya fara dawowa
Hukumar CDCFIB ta sanar a baya cewa masu neman aiki za su iya fara duba shafin tantancewa tun daga ranar Alhamis.
Dubban masu nema aikin sun koka da cewa suna fuskantar matsaloli kamar rashin iya shiga shafin, nuna musu mukamin da ba su nema ba, da kuma tsaikon aiki a shafin gaba ɗaya.
Sai dai binciken da jaridar Vanguard ta gudanar da safiyar Juma’a ya nuna cewa an fara samun sauyi a shafin, inda wasu da suka gaza shiga a baya yanzu suka fara iya shigar bayanan su.

Source: Twitter
Wani mai suna, Faisal Musa, ya shaidawa Legit Hausa cewa tun aafe yake kokarin shiga shafin domin duba sunansa amma har yanzu abin ya ci tura.
"Na yi iya bakin kokari na amma abin ya ci tura, ina ganin matsalar daga shafin ne, idan ya bude na saka bayanai na kamar yadda suka bukata, ba ya wucewa," in ji shi.
Amma wani Muhammad Bello da ya cike aikin hukumar shige da fice ya ce da safiyar yau Juma'a ya shiga shafin kuma bai ga wata matsala.
Ya ce yana sanya lambar katin dan kasa (NIN) da lambar wayarsa, shafin ya bude amma dai babu sunansa a cikin wadanda suka tsallake wannan matakin.
Gwamnati ta bude cibiyoyin samar da aiki
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da cibiyoyin samar da aiki domin rage rashin aikin yi tsakanain matasan kasar nan.
Karamar Ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce hakan na daga cikin manyan tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu da ke da nufin hada masu neman aiki da damar aiki kai tsaye.
Onyejeocha ta bayyana cewa cibiyoyin za su hada ayyuka da dama ciki har da bincike ta hanyar fasahar zamani, bin diddigin bayanan masu neman aiki da bayar da shawarwari kan aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

