Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Sanya Harajin 15% da zai Jawo Tashin Farashin Fetur

Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Sanya Harajin 15% da zai Jawo Tashin Farashin Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta kare sabon matakin da ta dauka na kakaba harajin 15% a kan man fetur da dizel da ake shigowa da su cikin kasar nan
  • Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa ƙara harajin shigo da mai da dizel zuwa 15 % wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa masana’antar mai ta gida
  • Mashawarcin Shugaban kasa na musamman a kan yada labarai, Sunday Dare ya ce tsarin zai rage dogaro da shigo da mai daga kasashen waje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bayyana cewa akwai hikima a cikin sanya harajin 15% a kan dukkanin man fetur da dizel da za a rika shigowa da su kasar nan.

Mashawarcin shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labarai, Sunday Dare ya ce wannan wani muhimmin mataki ne da zai sauya tsarin makamashi a ƙasar.

Kara karanta wannan

Yadda farashin fetur zai kasance bayan Tinubu ya amince da harajin 15% a Najeriya

Gwamnati ta kare matakin kara harajin fetur
Hoton Shugaban Kasa Bola Tinubu da Dangote Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

A sanarwar da ya wallafa a shfinsa na X, Sunday Dare, ya bayyana cewa an sanya harajin ne don rage dogaro kan mai da ake shigowa da shi daga waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban kasa ta kare harajin mai

A cikin sakon, Sunday Dare ya bayyana cewa muhimmin matakin zai kara tallafa wa masana’antar sarrafa mai ta gida da samar da ayyukan yi.

Mista Dare ya ce dogaro da mai da ake shigo da shi yana ta ƙara rage damar samar da ayyukan yi masu yawa, duk da cewa Najeriya tana daga cikin manyan masu hakar mai a duniya.

Gwamnati ta ce an sanya haraji domin bunkasa kasuwar mai
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Yanzu, ya ce, sabon harajin zai kawo canji ta hanyar ƙarfafa masana’antun ckin gida, haɓaka da tabbatar da an ci moriyar arzikin man fetur a cikin Najeriya.

Gwamnatin tarayya: 'Za a habaka matatun Najeriya'

A cewar Dare, wannan harajin zai rage sha'awar man da ake shigowa da shi cikin kasar nan, tare da bunkasa matatun mai irin na Dangote da sauransu.

Kara karanta wannan

Harajin 15%: Tinubu ya saka kudin shigo da fetur da dizil, mai na iya kara tsada

A kalamansa:

"An ƙirƙiri wannan sabon mataki ne don ƙarfafa sarrafa mai a cikin gida, haɓaka ƙarfin masana’antu na cikin ƙasa, da tabbatar da cewa kasa ta amfana da arzikin man Najeriya."
"Gwamnati tana karkatar da kasuwa zuwa ga amfanin masana’antun sarrafa mai na cikin gida kamar Dangote da sauran ƙananan masana’antu, domin shimfiɗa tubalin gina masana’antar makamashi mai ɗorewa da ƙarfi a kasar nan."

Gwamnatin ta jaddada cewa wannan mataki ba nauyi bane ga talakawa, sai dai gada ce daga dogaro da mai daga kasashen ketare.

Tinubu ya sanya harajin shigo da fetur, dizel

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da dora harajin 15% a kan shigo da man fetur da dizel daga ƙasashen waje, lamarin da ake ganin zai jawo hauhawar farashi.

An tura takardar amincewa ga Babban Lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi, Shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji, da kuma Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed domin aiwatar da tsarin.

Kara karanta wannan

'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda

A cewar takardar gwamnatin, an sanya harajin ba da nufin ƙara kudin shiga ba sai dai domin daidaita farashin man da ake shigo da shi tare da kare masana’antun tace mai na cikin gida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng