Yan Bindiga Sun Sace Masu Ibada 20, Sun Hallaka Malamin Addini a Kaduna
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kuma kai hari a Kaduna, suka yi garkuwa da mutane da dama yayin farmakin
- Cocin HEKAN a jihar Kaduna ya tabbatar da kashe wani babban Fasto tare da sace mutane sama da 20 a sanadiyyar harin miyagun
- Harin ya faru ne a Farin Dutse da ke karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna inda Faston ya rasa ransa bayan fitiwa daga maboyarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Karu, Kaduna - Cocin 'United Church of Christ in Nigeria' (HEKAN) ya bayyana damuwa kan kashe ɗaya daga cikin fastocinsa
An tabbatar da cewa Fasto Yahaya Kambasiya ya rasa ransa bayan wani harin yan bindiga da ya faru a jihar Kaduna.

Source: Original
An hallaka Fasto, an sace mutane a Kaduna
Vanguard ta tabbatar da cewa an kuma sace mutane fiye da 20 a mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Farin Dutse, ƙaramar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
Kwamandojin 'yan bindiga sun kaure da fada, shedanin dan ta'adda ya sheka barzahu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun nuna cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, inda ’yan bindigar da ke ɗauke da makamai suka mamaye garin, suna harbi ba kakkautawa, lamarin da ya jefa mazauna cikin firgici.
Shugaban cocin, Fasto Amos Kiri, ya bayyana harin a matsayin “rashin imani,” yana mai cewa an dade ana kai hare-hare kan al’umman Kiristoci a yankin.
A cewar rahoton, shugaban HEKAN a Kauru, Fasto Dauda Gambo, ya ce:
“Fasto Kambasiya da wasu sun buya a gona. Bayan sun zaci ’yan bindigar sun tafi, sai ya fito, aka harbe shi a baya, harsashi ya fito ta kirjinsa nan take.”
Yawan hare-hare a yankin Farin Dutse
Cocin ya tabbatar da cewa gawar marigayin ta kai asibiti, inda ake shirin birne shi tare da shawarar iyalansa.
HEKAN ta tuna cewa a Disamba 2024, an sace mutane 50 ciki har da Fasto Francis Lawal wanda daga bisani ya rasu a hannun masu garkuwa.
Hakazalika, a Oktoba 19, 2025, an sace mambobi hudu na cocin Kakude, wadanda har yanzu suna hannun masu garkuwa.
Fasto Kiri ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen kubutar da wadanda aka sace da kuma kawo ƙarshen wannan zalunci, yana mai cewa “iyalan wadanda abin ya shafa suna cikin tsananin baƙin ciki da tashin hankali.”
Ya kuma roƙi al’ummar Najeriya su yi addu’a don iyalan da abin ya shafa da kuma zaman lafiya a ƙasar, yana cewa:
“Muna roƙon Allah ya kawo ƙarshen kashe-kashe da sace-sacen mutane a ƙasarmu.”
Cocin ya bayyana cewa sun sanar da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da rundunar ’yan sanda a Kauru game da lamarin domin ɗaukar mataki, cewar TVC News.
Yan bindiga sun farmaki yan sanda a Kaduna
An ji cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda a garin Zonkwa, karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Jami’ai biyu na rundunar ‘yan sandan sun rasa rayukansu yayin da 'yan bindigar suka bude masu wuta a yankin.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne domin ’yantar da wasu masu laifi da 'yan sanda suka kama a Kachia.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
