Sojoji 2 Sun Tsallaka zuwa Ketare yayin da Ake Nemansu kan Zargin Juyin Mulki
- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami’ai biyu sun tsere bayan sun shiga cikin jerin wadanda ake zargi da shirin juyin mulki
- Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an da suka tsere sun hada da wani Manjo daga jihar Taraba da kuma daya daga birnin tarayya Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa sama da jami’an soja 30 yanzu suna tsare da ake bincike kan zargin juyin mulki wanda ya ta da hankula a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An gano cewa wasu jami’an soji biyu suna gudun hijira bayan an ambace su cikin wadanda ake zargi da shirin juyin mulki.
A kwanakin nan, ana zargin wasu sojoji da suka hada baki domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu da kuma dimokuradiyyar Najeriya.

Source: Twitter
Rahoton TheCable ya tabbatar da cewa ana neman sojojin guda biyu ruwa a jallo domin ci gaba da bincikensu kan abin da ake zarginsu.

Kara karanta wannan
EFCC ta kaddamar da binciken wadanda ake zargi da shirya kifar da Gwamnatin Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Juyin mulki: Ana binciken sojoji 16 da ake zargi
Majiyoyin tsaro sun ce jami’an sun tsere ne bayan rundunar soji ta kama wasu jami’ai 16 a farkon watan Oktobar 2025.
Hakan ya biyo bayan zargin sun yi yunkurin yin juyin mulki wanda ya gaza samun nasara duk da cewa rundunar tsaro ta musanta hakan.
Majiyoyi sun bayyana cikakken bayani kan sojoji 16 da ake zargi wanda ake tunanin shi ne dalilin sauya hafsoshin tsaro.
Rahotanni sun nuna sojoji 14 sun fito ne daga Rundunar sojojin kasa, sai kuma daya daga sojojin ruwa, yayin da ɗaya ya fito daga sojojin sama.

Source: Getty Images
Sojoji 2 da ake zargin sun tsere zuwa ketare
An bayyana cewa jami’an da suka gudu sune Manjo JM Ganaks, mai lamba N/14363 daga Abuja wanda ke aiki a Jaji a Kaduna.
Sai kuma Kyaftin G. Binuga, mai lamba N/167722 daga jihar Taraba wanda ke aiki a rundunar tsaro ta SOF a Bida da ke Jihar Neja.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki
Rahotanni sun nuna cewa bayan an kama wadanda ake zargi na farko, wasu daga cikinsu sun bayar da bayanai masu amfani, lamarin da ya taimaka wajen kama karin jami’ai har zuwa mutum 30.
Sai dai rundunar soji ta ƙaryata rahoton cewa juyin mulkin an shirya aiwatar da shi a ranar 1 ga Oktobar shekarar 2025.
Har ila yau, ta tabbatar da cewa binciken da ake yi yanzu bai da alaka da jita-jitar, hakan na cikin tsarin cikin gida ne don tabbatar da biyayya da ƙwarewa a rundunar.
Ana zargin an umarci soja ya hallaka Ribadu
Mun ba ku labarin cewa bayanai sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike game da yunkurin juyin mulki a Najeriya wanda ya sanya fargaba a cikin al'umma.
An ce an umarci wani jami’in sojojin sama da aka tura ofishin Nuhu Ribadu ya kashe shi kafin zargin juyin mulki ya faskara.
Hedikwatar tsaro ta ce bincike yana gudana yayin da gwamnati ta yi garambawul ga manyan hafsoshin tsaro kwanakin baya domin inganta tsaron kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng