Gumi Ya Goyi bayan Yiwa Maryam Sanda Afuwa, Ya ce ba a Saba Dokar Musulunci ba
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce kashe Maryam Sanda ba shi ne zai zama adalci ba bayan an same ta da kashe mijinta
- A cikin wani karatunsa, Malamin ya bayyana cewa yafiya a Musulunci tana da daraja fiye da ramuwar gayya
- Dr. Ahmed Gumi ya kuma yabi mahaifin Bilyaminu Bello da ya yafe jinin ɗansa da matarsa, Maryam ta kashe
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, ya bayyana cewa kashe Maryam Sanda ba shi ne adalci na gaskiya ba.
Ya bayyana cewa afuwar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi mata tafi dacewa da koyarwar Musulunci.

Source: Facebook
A sakon da wani da ake kira Izala ya wallafa a shafin X, Sheikh Gumi ya yi wannan bayani ne yayin tafsirin karatunsa na mako-mako kan littafin Risāla na Imam Abdullahi Ibn Abi Zayd Al-Qairawani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmad Gumi ya magantu kan yafewa Maryam Sanda
Karatun Shaikh Gumi na makon ya fado a babin da ya shafi Qisas – wato hukuncin ramuwar gayya da yafiya a Musulunci a daidai lokacin da ake takaddama kan batun Maryam Sanda.
Yayin da yake magana kan shari’ar Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa saboda kisan mijinta, Gumi ya ce:
“Sun ce ta soki mijinta, sannan ta fashe da kuka a kansa. Wannan aikin shaidan ne. Daga yi mata afuwa, mutane suka fara magana ba tare da sani ba, suna mantawa da dokar yafiya a Musulunci.”
Ya ƙara da cewa:
“Iyalin wanda aka kashe sun ce ‘mun yafe mata’. Allah Ya kiyaye mu gaba ɗaya.”
Sheikh Gumi ya yi bayanin yafewa Maryam Sanda
Sheikh Gumi ya bayyana cewa irin wannan yafiya da iyalan mamacin suka bayar tana da matsayi mafi girma a Musulunci.
“A Musulunci, idan iyalin wanda aka kashe sun yafe, ba rauni ba ne – rahama ce, kuma rahama tafi soyuwa a wurin Allah fiye da ramuwar gayya.”

Kara karanta wannan
Lauya ya fadi lokacin da ya ragewa Maryam Sanda a kurkuku sakamakon afuwar Tinubu
Sheikh Gumi ya jaddada cewa kisan Maryam ba zai zama mafita ba, domin a Musulunci adalci yana kan daidaito da tausayi, ba fushi ko son zuciya ba.

Source: Facebook
A Kalamansa:
“Afuwar shugaban ƙasa da aka bayar ita ce daidai. Adalci ba fushi ba ne – adalci da tausayi ne."
Rahoton ya tunatar da cewa shari’ar Maryam Sanda ta samo asali ne daga mutuwar mijinta Bilyaminu Bello a ranar 19 ga Nuwamba, 2017, bayan saɓani da suka samu a gidansu da ke Maitama, Abuja.
Kotun babban birnin tarayya ta same ta da laifin kisa ta kuma yanke mata hukuncin kisa a 2020 kuma motun daukaka kara da kuma kotun koli sun tabbatar da hukuncin.
Amma a wannan shekara ta 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu sanya ta a cikin wasu fursunoni da ya yiwa afuwa.
Dr. Ahmad Gumi ya shawarci alkalai
A baya, mun wallafa cewa Sheikh Ahmad Gumi ya shawarci alƙalan Musulunci da malamai su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci ga matan da ake zalunta a gidajen aure.
Ya bayyana cewa dole ne a ba mata damar neman rabuwar aure ba tare da fansar kansu ba idan zaman aure ya gagara, musamman ma idan an nuna cewa an zalunce su.
Sheikh Gumi ya jaddada cewa ana gina a Musulunci ya tausayawa, mutunta juna da jinƙai, tare da nanata cewa addinin Musulunci bai yarda ma'aurata su rika wulaƙanta junansu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

