'Yan Ta'adda da ke da Alaƙa da Al Qaeda Sun Kai Harin Farko a Arewacin Najeriya

'Yan Ta'adda da ke da Alaƙa da Al Qaeda Sun Kai Harin Farko a Arewacin Najeriya

  • Kungiyar ta'addanci ta JNIM da ake dangantawa da Al-Qaeda ta ce ita ta kai harin farko a Arewacin Najeriya
  • Ta kai harin a karon farko watanni bayan ayyana sabuwar rundunarta a Najeriya wanda ke kara barazanar tsaro a kasar
  • Rahotanni sun nuna harin ya faru a Arewacin Kwara wacce ke da iyaka da Kogi da Najeriya da Nijar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Kungiyar ta'addanci ta Jama’at Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin (JNIM) da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin wani hari a Arewacin Najeriya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa kungiyar ta kai ne a Jihar Kwara, wanda shi ne na farko a Najeriya bayan ayyana alaka da JNIM.

Sabuwar kungiya ta kai harin ta'addanci a Kwara
Taswirar jihar Kwara inda ake fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da harin a yau Alhamis 30 ga watan Oktobar 2025 a shafin X.

Kara karanta wannan

Kwamandojin 'yan bindiga sun kaure da fada, shedanin dan ta'adda ya sheka barzahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jihar Kwara ta fada matsalar tsaro

Jihar Kwara na daga cikin jihohi a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya da ke fama da matsalar tsaro wanda ke jawo nakasu ga ci gaban jihar.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya sha yin alwashi kan matsalar inda ya ke cewa zai kawo karshen dukan matsalolin da jihar ke fuskanta.

Sai dai har zuwa yanzu babu wani sauyi yayin da yan ta'addan ke ci gaba da cin karensu babu babbaka da ya bar al'umma cikin zullumi ba tare da sanin makomarsu ba.

Gwamna AbdulRazak ya damu da matsalar tsaro a Kwara
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government.
Source: Facebook

Yan ta'addan sun farmaki Kwara a karon farko

Bayanan leken asiri sun ce harin ya faru a Arewacin Kwara, kusa da iyakar da ya haɗa jihar da Kogi da Nijar a yankin.

JNIM, wacce ta fi tasiri a Mali da Burkina Faso da Nijar, ta sanar a watan Yunin 2025 cewa ta kafa sabuwar runduna a Najeriya.

Rahotanni sun ce wannan lamari ya zo a lokacin da ake gargaɗin na shigowar mayaƙa ta hanyar fasa-kwauri da ke tsakanin Jamhuriyar Benin da Nijar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

Majiyar tsaro ta ce:

“Idan wannan ta tabbata, zai nuna sabon yanayi na matsalar tsaro a yankin."

Shawarar da aka ba hukumomin tsaro

An shawarci hukumomin tsaro a Kwara da Kogi da su ƙara sintiri da sa ido, tare da tura jami’ai zuwa yankunan iyaka domin tabbatar da tsaron al'umma baki daya.

Sojoji da hukumar leken asiri za su binciki yiwuwar haɗin kai tsakanin mayaƙan JNIM da ƙungiyoyin ta’addanci na cikin gida a Najeriya.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake fama da rashin tsaro a yankin Sahel da yawaitar ƙananan ƙungiyoyin ta'addanci da ke kai hare-hare.

Gwamna Sule ya bayyana bullar kungiyar ta'addanci

A baya, kun ji cewa Gwamnan Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gargadi jama’a kan bullar wata sabuwar kungiyar ta'addanci.

Gwamna ya nuna damuwa kan kungiyar da ya yi zargin wani ɓangaren Boko Haram ne da suka kwararo yankin domin ci gaba da kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta na iya ƙara lalata tsaro, musamman ganin yadda ‘yan Lakurawa suka riga suka bazu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.