An ‘Gano’ Sojan da Aka Tura Ya Hallaka Ribadu a Zargin Yunkurin Juyin Mulki
- Bincike na ci gaba da tono bayanai kan zargin wasu sojoji da ake hasashen sun yi yunkurin juyin mulki a Najeriya
- Majiyoyi suka ce an gano wani jami’in sojojin sama da aka tura ofishin Nuhu Ribadu da umarnin ya kashe shi
- Hedikwatar tsaro ta ce bincike yana gudana yayin da gwamnati ta yi garambawul ga manyan hafsoshin tsaro kwanakin baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike game da yunkurin juyin mulki a Najeriya wanda ya sanya fargaba a cikin al'umma.
An ce an umarci wani jami’in sojojin sama da aka tura ofishin Nuhu Ribadu ya kashe shi kafin zargin juyin mulki ya faskara.

Source: Facebook
Rahoton TheCable ya ce an tura SB Adamu mai lamba NAF/3481 daga Jigawa, NCTC karkashin ofishin Ribadu sati hudu kafin abin ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin shirin juyin mulki a Najeriya
Wannan zarge-zarge na zuwa ne yayin da ake ganin wasu sojoji sun shirya kifar da gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya.
Sai dai tun da wuri, rundunar tsaro ta musanta hakan inda ta kuma ce babu alakar hakan da soke bikin ranar yancin kasa.
Ana kan haka, sai aka ci karo cewa ana tuhumar sojoji 16 kan laifuffuka daban-daban, amma rundunar ta ce binciken ba shi da alaƙa da zargin yunkurin juyin mulki a kasar.
Yadda aka tura soja ofishin Nuhu Ribadu
Rahotanni sun tabbatar da cewa Adamu shi kaɗai ne daga ofishin da ake zargi da hannu, duk da bayanai sun nuna cewa jami'ai da yawa suna aiki a ofishin.
Kwamandan NCTC, Janar Adamu Garba Laka, ya nemi wani jami’i daban a watan Agusta, amma sai aka tura SB Adamu ofishin.

Source: Twitter
Zargin da ake yi kan sojan sama

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Wannan lamari ya haddasa zargin cewa masu juyin mulki sun samu damar rabar manyan jami'an tsaro.
An ce Adamu na cikin sahun 'yan aji na 59 a NDA, kuma yana taimakawa wajen binciken lamarin, bisa bayanan da aka samu.
Shugaba Tinubu kwanan nan ya sallami manyan hafsoshin tsaro, ciki har da Air Marshal Hasan Abubakar, kafin rahoton nan ya bayyana.
An ce Adamu ya samu umarni na musamman don "kashe" Ribadu, sai kuma wasu sojoji su hallaka wasu manyan jami’an gwamnati.
Meye rundunar tsaro ta ce kan zargin sojoji?
Har yanzu hukumomin sojoji ba su fitar da bayani a hukumance ba, kan lamarin juyin mulki da ake zargi da jami’an 16.
Rundunar tsaro ta ce binciken cikin gida ne domin tabbatar da bin tsari, kuma za a fitar da sakamakon a bainar jama’a in an kammala.
Juyin mulki: Bayani kan sojoji da ake zargi
A wani labarin, an ji rundunar tsaro na ci gaba da binciken manyan sojoji 16 kan zargin shirin juyin mulki a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a Najeriya.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Yadda sojojin da aka tsare suka 'tona asirin' tsohon minista, Timipre Sylva
Majiyoyi sun bayyana cikakken bayani kan sojojin da ake zargi wanda ake tunanin shi ne dalilin sauya hafsoshin tsaro.
Rahotanni sun nuna sojoji 14 ne daga Rundunar sojojin kasa, ɗaya daga Sojojin Ruwa, da kuma ɗaya daga sojojin Sama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
