Kwamandojin ’Yan Bindiga Sun Kaure da Fada, Shedanin Dan Ta’adda Ya Sheka Barzahu

Kwamandojin ’Yan Bindiga Sun Kaure da Fada, Shedanin Dan Ta’adda Ya Sheka Barzahu

  • Wani daga cikin fitaccen kwamandan ’yan bindiga ya rasa ransa yayin rikici da abokan gaba a jihar Katsina
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu sabani ne tsakaninsu kan ikon wani yanki wanda ya yi silar kai hare-hare
  • Dan bindiigan ya shahara da kai hare-hare, sace mutane, da satar dabbobi, har ma yana TikTok da nuna makamai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutsenma, Katsina - Wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga a jihar Katsina ya bakunci lahira lahira bayan arangama da abokin adawarsa.

Dan ta'addan da aka fi sani da Jankare ya rasa ransa a hannun wata kungiya ta abokan ta’addanci, sakamakon rikici mai zafi.

An hallaka kwamandan yan bindiga a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalolin tsaro a Arewa. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama a X ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yankin Dutsenma na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga ke hallaka junansu

Ana yawan samun arangama tsakanin yan bindiga da ke kai hare-hare saboda wasu dalilai na su na karan kansu a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Ko a jihar Zamfara ma, jagoran yan ta'adda, Kachalla Abu Dan Barka, da wasu mayaƙansa sun mutu a harin abokan gaba a karamar hukumar Maru da ke jihar.

An ce an kashe Dan Barka ne da mayaƙansa lokacin da aka yi musu kwanton-bauna a yankin Dansadau.

Hakan na kara ragewa rundunar sojoji aiki yayin da suke kokarin kakkabe yan ta'addan domin tabbatar da samar da zaman lafiya da kare dukiyoyi da rayukan al'umma.

Hatsabibin dan bindiga ya sheka barzahu a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda da dan bindiga, Jankare. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda, @ZagazOlamakama.
Source: Facebook

An hallaka dan bindiga a artabu a Katsina

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan sabon rikici ya kunno kai tsakaninsa da wani kwamandan ’yan bindiga.

Hakan bai rasa nasaba da yadda ake gudanar da miyagun ayyuka da kuma iko kan yankunan.

Kara karanta wannan

Taraba: Rigima ta barke kan mallakar Masallacin Juma’a na Izalah, an rasa rai

An ce Jankare, wanda ya shafe lokaci mai tsawo yana tsoratar da al’umma a Dutsenma da wasu yankunan makwabta, an harbe shi a lokacin artabun.

Shaidar da aka yi wa Jankare a Katsina

Jankare ya shahara da jagorantar hare-hare masu muni, sace mutane, da satar shanu a yankin.

Haka kuma ana yawan ganinsa a TikTok yana nuna makamai, yana cin mutuncin hukumomin tsaro.

An bayyana cewa kwanan nan ya halarci wani taron da manyan ’yan bindiga suka shirya domin warware sabani da tsara sabbin hare-hare, kafin rashin jituwa tsakaninsa da abokan ta’addanci ya kai ga kashe shi.

Sai dai bayan mutuwarsa, jami’an tsaro na bibiyar lamarin sosai, domin kauce wa yiwuwar ramuwar martani tsakanin kungiyoyin ’yan bindiga da ke fafatawa a yankin.

Yan bindiga sun saki mutane 19 a Katsina

Mun ba ku labarin cewa al'ummar jihar Katsina na ci gaba da ganin amfanin sulhu bayan wasu tubabbun yan bindiga sun sako mutane.

'Yan bindigar sun saki mutum 19 da suka yi garkuwa da su a Katsina, bayan tattaunawar zaman lafiya karkashin shirin 'Operation Safe Corridor'.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun farmaki masu sallah, sun yanke kan wani da ke kokarin tserewa

Hukumomi suka ce ana duba lafiyar wadanda aka sako a cibiyar lafiya ta Haske, Sabuwa, kafin maida su wurin iyalansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.