'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu Mutane bayan Kai Hari a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu Mutane bayan Kai Hari a Sokoto

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto
  • Tsagerun sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da yin awon gaba da wasu mutane daban
  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce jami'anta sun ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - ‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Kurawa da ke cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kashe mutane uku ciki har da mai rikon kwaryar sarautar kauyen a yayin harin da suka kai.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu da Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun Hoto: @AhmedAliyuskt, @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce maharan sun mamaye kauyen ne da sanyin safiyar Alhamis, inda suka kuma sace wasu mazauna kauyen tare da shanu 40.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda sojojin da aka tsare suka 'tona asirin' tsohon minista, Timipre Sylva

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa maharan sun iso kauyen ne misalin karfe 12:00 na dare, bayan sun lalata wani ɓangare na katangar da al’umma suka gina domin kariya.

“Mun samu kiran gaggawa daga wani ƙauye da ke makwabtaka da mu cewa ‘yan bindiga suna tafe. Nan da nan muka sanar da hukumomi da jami’an tsaro."
“Sun shiga kauyen bayan sun lalata wani bangare na katangar sannan suka fara harbe-harbe ba kakkautawa."
“Harin bai kai mintuna 30 ba, sabanin na baya wanda kan ɗauki sa’o’i. Sai dai 'yan sa-kai da jami’an tsaro sun fafata da su."

- Wani mazaunin yankin

Duk da wannan kokari, mutane uku sun rasa rayukansu, ciki har da mai rikon kwaryar sarautar kauyen, Hussaini Alhaji Yawalle, da Haruna Alhaji Zuguru, inda aka birne gawarwakin su a ranar Alhamis.

A Sokoto, 'yan bindiga na yawan kai hare-hare

Kara karanta wannan

'Yan bindiga saman babura sun kai hari a Kano, an yi barna

Wani mazaunin yankin ya ce wannan ne hari na 20 da ‘yan bindiga suka kai wa kauyen tun farkon faruwar rikice-rikicen tsaro a yankin.

“Shi ya sa muka yanke shawarar gina katanga domin kariya, amma ba mu yi tsammanin za su iya lalata ta ba."
“Sun sace mutane da dama ciki har da tsohon malamin makaranta, Malam Abdullahi, sannan suka yi awon gaba da shanu fiye da 40.”

- Wani mazaunin yankin

Ya bayyana harin a matsayin babban rashi ga al’umma, yana mai cewa waɗanda suka mutu fitattun mutane ne da suka taka muhimmiyar rawa wajen kare kauyen.

'Yan sanda sun kai dauki

Legit Hausa ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

'Yan sanda sun kai dauki a Sokoto
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kakakin 'yan sandan ya tabbatar da kashe mutane uku amma bai bada tabbacin cewa cikinsu akwai mai rikon kwaryar sarautar kauyen ba.

Ya bayyana cewa 'yan bindigan sun sace mutane bakwai, kuma jami'ansu tare da hadin gwiwar sojoji sun ceto mutane shida daga cikinsu.

"Bayan samun rahoton, an tura jami'an 'yan sanda da sojoji wadanda suka samu nasarar ceto mutane shida daga cikin mutane bakwai da aka sace."

Kara karanta wannan

Sulhu ya yi rana: Tubabbun 'yan bindiga sun sako mutane makonni da sace su

- DSP Ahmed Rufai

''Yan bindiga sun kakaba haraji a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindga sun sanya harajin miliyoyin Naira ga mutanen kauyen Bazar a jihar Sokoto.

Mutanen kauyen wanda yake a karamar hukumar Yabo sun mika kokon bararsu ga gwamnati kan ta kawo musu dauki.

Sun bayyana cewa idan ba su biya kudin ba, akwai yiwuwar ‘yan bindigar su kai musu hari ko su lalata amfaninsu da ke gona, wanda hakan zai iya jefa su cikin tsananin talauci da yunwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng